Mummunan bala′i a tsibirin Lampedusa | Siyasa | DW | 04.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mummunan bala'i a tsibirin Lampedusa

Hadarin jirgin ruwan 'yan gudun hijira da ya yi sanadiyar rayukan daruruwan mutane a kusa da gabar tekun kasar Italiya shi ne irinsa mafi muni.

Hadarin jirgin ruwan da ya taso daga Libya kuma ya ke dauke da kimanin mutane 500 wanda suka kunshi 'yan Somaliya da Eritrea ya faru ne bayan da wuta ta kama lokacin jirgin da ke dab da isa gabar ruwan Lampedusa, lamarin da ya sanya shi kifewa inda nan take mutane 94 ciki har da mata da yara kanana suka rasu.

Rahotanni sun ce wasu masunta ne suka fara tsinkayar hadarin, inda suka shaida wa masu tsaron gabar ruwa na kasar Italiya wanda daga bisani suka fara aikin ceto wadanda ke da sauran numfashi inda suka samu nasarar kubutar da mutum sama da 150.

Duk da cewar ma'aikata sun kubutar da wasu da ransu, kawo yanzu ba a ji duriyar wasu mutane sama da dari biyu ba, wannan ne ma ya sanya ministan da ke kula da harkokin wajen Italiya Emma Bonino cewar aikin ceto ya ci karo da kalubale wanda rashin kyauwun yanayi da ake fama da shi yanzu haka a tsibirin ke dada dagula shi.

Damuwa ga yawaitar hadari a Bahar Rum

Da ta ke tsokaci dangane da hadarin, shugabar hukumar gudanawar garin Lempedusa Guisi Nicolini cewa ta yi abu ne mai tada hankali matuka, inda a hannu guda ta nuna damuwarta ta rashin fara aikin ceto cikin gaggawa.

"Ina son sanin dalilin da ya sanya masu sitiri kan gabar ruwan tsibirin ba sa kusa lokacin da hadarin ya faru, lallai akwai wani kuskure wanda ni ban fahimta ba."

Wannan hadari da ma wanda ya faru kwanakin bayan nan a tsibirin Sicilly na kasar ta Italiya ya sake bijiro da korafin da shugaban kasar Giorgio Napolitano da ma sauran al'ummar Italiya ke yi na cewar kasashen Turai sun kyale Italiya na fama da wannan matsala ita kadai maimakon a dafa mata don kawo karshen asarar rayukan da ake, musamman ma dai wajen yin sunturi a yankunan arewacin Afirka da nufin taka burki ga bakin haure da ke kokarin zuwa Turai ta jiragen ruwa.

Shi ma dai ministan cikin gidan Italiyan Angelino Alfonso cewa ya yi lokaci ya yi da kasashen Turai za su matsa kaimi wajen kaiwa ga magance wannan ibtila'i da ke cigaba da faruwa domin kuwa Lampedusa ba wai ta Italiya ba ce ita kadai, mashiga ce ta kasashen Turai kamar dai yadda ya shaida a wani jawabi da ya yi ga manema labarai jim kadan bayan aukuwar hadarin.

Italiya na bakin kokarinta

Wannan ne ma ya sanya daraktan cibiyar bincike ta kasa da kasa kan bakin haure Ferrucio Pastore cewar ya kamata a jinjinawa kasar ko da ya ke mafi akasarin aikin ceton ba jami'an gwamnati ne ke yi ba.

"Galibin jiragen da ke fara ceton ba sojin ruwan kasar ko na masu gadin gabar ruwa ba ne, mafi yawanci na masunta ne kuma suna bukatar a tallafa musu domin aikin na da wuya da tsadar gaske."

Duk da yawan hadarin da ake samu na jiragen ruwan 'yan gudun hijirar Afirka da ke kokarin shigowa Turai ta ruwa, bai sa guiwar wasu matasan Afirka da ke son shigowa Turai don samun wata rayuwa mai inganci ta karaya ba.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin