1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mulkin kama-karya na karuwa a kasashe masu tasowa

Jens Thurau Suleiman Babayo/Mouhamadou Awal Balarabe
March 19, 2024

Binciken Gidauniyar Bertelsmann ta Jamus ya nunar da cewar mulkin kama-karya ya yadu a kasashe 74 masu tasowa. Sai dai shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce akwai bukatar tashi tsaye don kare dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/4duPd
 Shugaban mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss Deby ya tube kaki don tsayawa takara
Shugaban mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss Deby ya tube kaki don tsayawa takaraHoto: Denis Sassou Gueipeur/AFP

Sabon binciken Gidauniyar Bertelsman ya ce adadin kasashen da ba a samun ingancin dimukuradiyya na karuwa, inda ya nunar da cewar irin wannan salon mulki ya tabarbare a cikin shekaru 20 da suka gabata a kasashe 137 masu tasowa. Bisa ga kididdigar da gidauniyar ta fitar, yanzu akwai kasashe 63 da ke bin mulkin dimukuradiyya yayin da 74 ke gudanar da salon mulkin kama-karya, ma'ana kasashen da ba a gudanar da sahihin zabe ko kuma tsarin shari'arsu ke da nakasu.

Karin bayani: Guinea Conakry: Shakku kan alkawarin zabe

 Shugaban gwamnatin Jamus Scholz kewaye da jagororin gidauniyar Bertelsmann
Shugaban gwamnatin Jamus Scholz kewaye da jagororin gidauniyar BertelsmannHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Gidauniyar ta ma gayyaci shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz don gabatar da binciken, a daidai lokacin da tsananin akidar kyamar baki da ra'ayin mazan jiya ke karuwa a kasar. Scholz ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana jin dadinsa dangane da yadda dubban mutane suka fito kan tituna don kare dimukuradiyya tare da barranta kansu da jam'iyyar AFD da ke da wannan manufa. Dama bincike ya ce a cikin shekaru biyun da suka gabata, ba a gudanar da zabe mai inganci a kasashe 25 ba, bayan rabuwa da annobar Corona da kuma mamayar da Rasha ta yi wan Ukraine. Sannan a  kasashe 39, an kara tauye 'yancin fadin albarkacin baki.

Karin bayani: 2023: Shekara mai sarkakiya ga dakarun MDD a Afirka

Sabine Donner na daya daga cikin wadanda suka gudanar da bincike kan dimukuradiyya
Sabine Donner na daya daga cikin wadanda suka gudanar da bincike kan dimukuradiyyaHoto: Bertelsmann-Stiftung

Sabine Donner tana cikin wadanda suka rubuta wannan rahoton, inda ta ce: "Annobar Corona ta janyo jingine wasu ka'idodji na kare hakkin dan Adam na wani lokaci da suka shafi 'yancin walwala, inda haka ya shafi ci-gaban tsarin dimukuradiyya. Wannan annoba ta zama dama da aka yi amfani da ita wajen karbe 'yancin mutane da kara karfi ga gwamnatoci. Bisa manufa, wannan anonnba ba wata sabuwar matsala da ta kirkiro ba, da ma suna nan"

Karin bayani:Dimukuradiyya na cikin rikici a wasu sassa

A cewar wannan Gidauniya ta Bertelsmann, binciken da ta yi shi ne mafi girma da ya kunshi galibin abubuwan da ake bukata. Rahoton mai shafi dubu-biyar ya tattaru neda taimakon masana kimanin 300 daga jami'o'i 300 da cibiyoyin bincike a kasashe kusan 120. Ta dogara ne a kan rukunoni uku wajen nazartar yanayin dimukuradiyya da ci-gaban tattalin arziki da ayyukan gwamnati, duk da karancin tarihi da bincike da ata fuskanta.

Paul Biya na kamaru da Janar Eligui Nguema na Gabon na na cikin wadanda ke gudanar da mulkin kama-karya
Paul Biya na kamaru da Janar Eligui Nguema na Gabon na cikin wadanda gudanar da mulkin kama-karyaHoto: Mouhamadou Awal Balarabe/DW

Karin bayani: Barazana ga daular sarakuna a kasashen Larabawa

Sabine Donner wanda take ciki wanda suka rubuta rahoton na ganin cewar an yi sake wajen barin lamarin ya ta'azzara: "A shekaru biyu zuwa hudu da suka gabata, mutane da gwamnatoci gami da kasashe ciki har da Jamus, sun kara saka ido game da yiwuwar samun kalubalen tsarin kama-karya. Amma akwai wadanda suka samu karfin gwiwa fiye da shekaru 10 da suka gabata."

Rahoton ya nuna cewar har yanzu kungiyoyi masu zaman kansu na kokarin wajen ganin an tabbatar da tsarin zabe mai adalci da tabbatar da 'yancin kafofin yada labarai.