1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhimmancin shayar da jariri Nonon uwa

August 6, 2021

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da hukumar lafiya ta Duniya WHO sun bayyana damuwa kan yadda masu sarrafa abincin jarirai ke amfani da yanayin da aka shiga na annobar COVID-19 don cin kazamar riba.

https://p.dw.com/p/3yfJ6
Burundi Wahlen
Hoto: Berthier Mugiraneza/AP Photo/picture alliance

Asusun na UNICEF da hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna damuwa saboda yadda aka samu koma baya kan yadda ake shayar da yara Nonon uwa tsantsa a Najeriya duk da kokarin da ake yi na fadakar al’umma shayar da Nonon uwa maimakon abincin yara da kamfanonin ke sarrafawa.

A cewar hukumomi a Najeriya yara uku ne daga cikin goma suke samun Nonon uwa abin da ke nuna gagarumin koma baya a kokarin karfafa shayar da yara nonon uwa musamman a watanni shida na farkon rayuwar yaro.

Da ma kuma akwai iyayen da har yanzu basu yarda da shayar da Nonon uwa zalla ba watakila saboda gudun sauya yanayin jikin su ko kuma hada bada Nonon da ruwa ko wani abinci da sunan  nuna tausayi ga yaran. Malama A’isha Muhammad wata uwa ce da ta ce ba za ta iya bai wa dan ta nono zalla ba sai ta hada da ruwa.

Masu rajin tabbatar da shayar da yara nonon uwa kamar Nasir Musa wanda aka fi sani da Dr Naseef na zargin Kamfanonin da ke sarrafa abincin yara da yaudara don sayar da hajar su.

Yanzu haka gwamnatoci na yin bakin kokarin wajen karfafa fadakar da mutane muhimmancin shayar da nonon uwa ga yara domin amfanin sa.

Yanzu haka dai akwai iyaye da suke yaye da ‘ya‘yansu da sunan yaki da annobar COVID-19 abin da ya sa wasu kamfanonin sarrafa abincin yara suke amfanin wannan dama wajen sayar da kayayyakinsu lamarin da ya sa hukumomi nuna damuwa.