Puigdemont ya goyi bayan Torra a Kataloniya
May 11, 2018Talla
A wannan Asabar din ce 'yan majalisar dokokin yankin Kataloniya za su yi muhawara kan ko za su amince da me goyon bayan shirin ballewa daga kasar Spain Quim Torra, don shugabantar yankin bayan da tubabben shugaban yankin Carles Puigdemont ya janye daga neman shugabanci ya nuna goyon bayansa ga Torra.
Bayan tattaunawa da jam'iyyu da dama kakakin majalisar ta Kataloniya Roger Torrent a hukumance ya bayyana Torra a matsayin dan takarar shugabancin yankin na Kataloniya inda ya kira zaman majalisar ranar Asabar kamar yadda jawabin da ya fito daga majalisar yankin ya nunar.