Muhawara dangane da harin Boston na Amirka | Siyasa | DW | 22.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Muhawara dangane da harin Boston na Amirka

Takaddama ta kunno kai a tsakanin masana dangane da ko harin Boston na ta'addanci ne ko kuma na manyan laifuka ne.

Zargin da hukumomin tsaron Amirka ke yiwa wani dan asalin Ceceniya na alhakin hari da aka kaddamar akan 'yan gasar tseren nisan zango a Boston, ya tada sabuwar muhawara dangane da na'uin shari'ar da zai fuskanta.

Cece kucen daya kunno kai a tsakanin kafofin yada labaran Amirka tun bayan nasarar da jami'an hukumar leken asirin kasar ta FBI suka yi na cafke Dzhokar Zarnajew dai na da nasaba ne da ko zargin da ake yi masa na alhakin kai harin na karkashin dokokin da suka shafi manyan laifuka ne a kasar ta Amirka, wanda ke nuna bukatar gurfanar da shi a gaban kotun shari'ar manyan laifukan, ko kuma a'a ya shafi laifukan ta'addanci ne, wanda ke nuna bukatar gurfanar da shi a gaban kotun soji.

Batun harin na Boston dai ya tado da zazzafar muhawara dangane da dacewar siffanta Dzhokar Zarnajew a matsayin dan ta'adda da kuma gurfanar dashi a gaban kotun soji duk da cewar a yanzu yana da takardar shaidar zama dan kasar Amirka ne a hannu guda. Ga shi kuma a daya hannun, gurfanar da mutum a gaban kotun soji, ya shafi wanda dokokin Amirka ke dauka ne a matsayin makiyin da ke musayar wuta da jami'am tsaro, kwatankwacin wadanda Amirka ke ci gaba da garkamewa a gidan yarin Guantamo Bay.

Shin harin Boston na ta'addanci ne ko kuma a'a?

Sai dai kuma ko da Dzhokar Zarnajew zai fuskanci shari'a a gaban kotun fararen hula ne, amma sashen shari'ar Amika na tattara bayanai da nufin kammala shari'ar ta sa a karkarshin dokokin da suka shafi laifukan ta'addanci, wanda kuma Ralph Companion, darektan kula da cibiyar nazarin harkokin siyasa dana sadarwa a a jami'ar Deleware na kasar ta Amirka ya shaidawa tashar DW cewar, akwai abin dubawa game da siffanta, mutane biyun da ake zargi da harin na Boston da laifin ta'addanci:

Ya ce " Bam gamsu da siffanta wadannan mutane biyun da ake zargi da harin da cewar 'yan ta'adda ne ba, domin kuwa babu wani ta'addancin daya wuce na wanda ya kai hari a wata makaranbtar daya yi sanadiyyar mutuwar mutane 26, amma kuma ba a ce na ta'addanci ne ba, sai wannan. Sam sam ni ban amince da banbanta wadannan laifuka biyu ba."

Ko da shike a karkashin dokokin jihar Masachusset na Amirka dai babu hukuncin kissa, amma kuma a karkashin dokokin tarayya akwai hukuncin na kissa, lamarin da kuma ke nuna cewar Dzhokar Zarnajew zai fuskanci hukunci ne bisa la'akari da irin dokar da aka gurfanar dashi a karkashinta, wato na jiha ko kuma na tarayya.

Tasirin kafofi yada labarai a lokutan rigingimu

Baya ga batun dokar kuwa, takaddamar da ta kunno kai a yanzu ta shafi yadda kafofin yada labarai ke yada abinda Ralph Companion, darektan kula da cibiyar nazarin harkokin siyasa da na sadarwa a jami'ar Deleware na kasar ta Amirka ya bayyanawa DW da cewar bayanai amma ba labarai ba, kana kuma ba tare da tantance su ba:

Ya ce "Abin bakinci ne cewar, duk da cewar kafar sadarwa ta Internet ta baiwa mutane damar yin tsokaci da kuma yada bayanai, amma kuma ta baiwa wasu rukuni ma damar yada bayanai da kuma labarai marasa inganci."

Rashin ingancin labaran da kuma hotunan da ke tada hankulan jama'a ne ya sa masanin ya bayyana bukatar yin taka-tsantsan game da abubuwan da ake yadawa a shafukan sadarwar, domin kaucewa yanayi irin na Boston, inda a martanin da jami'an tsaro suka mayar, ya sa harkokin yau da kullum suka tsaya cik - da sunan binciken gano wadanda suka kai hari akan 'yan tseren nisan zango.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal

Sauti da bidiyo akan labarin