Mugabe zai fiskanci tsigewa a siyasance | Labarai | DW | 21.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe zai fiskanci tsigewa a siyasance

Jam'iyyar shugaban na Zimbabuwe a wannan rana ta Talata ta umarci mai tsawatarwa a majalisa ya ci gaba a gabatar da shirin tsige shugaban.

A wannan rana ta Talata ce jam'iyya mai mulki a kasar Zimbabuwe za ta kaddamar da fara shirin tsige Shugaba Robert Mugabe a majalisa, matakin da ke zama na baya-bayan nan a yunkuri na raba shugaban dan shekaru 93 daga kujerar mulki bayan kwashe shekaru 37 a kan ragamar kasar.

Jam'iyyar shugaban a wannan rana ta Talata ta umarci mai tsawatarwa a majalisa ya ci gaba a gabatar da shirin tsige shugaban, haka shi ma  shugaban rundinar sojan kasa Constantino Chiwenga ya ce tattaunawar tunbuke shugaba ta yi nisa.

Ya kuma kara da cewa Shugaba Mugabe na tuntubar mataimakinsa da ya kora Emmerson Mnangagwa. An dai ga zanga-zanga ta dalibai na jami'a da ke neman ganin Shugaba Mugabe ya taba kasa daga mulkin, yayin da a bangaren shugaban sojan kasar Chiwenga ya yi kira na a kwantar da hankula.