Mugabe ya sallami mataimakiyarsa | Labarai | DW | 09.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe ya sallami mataimakiyarsa

Joice Majuru dai da ake wa kallon wacce za ta iya gadar shugaba Mugaben na Zimbabwe ya zuwa yanzu shugaban ya sallame ta saboda zargin yi masa zagon kasa.

Joice Mujuru

Joice Mujuru: Mataimakiyar shugaba Mugabe da ya sallama

Shugaba Mugabe na Zimbabwe ya sallami mataimakiyarsa Joice Mujuru, kwanaki bayan da ta rasa kujerarta a jam'iyya mai mulki, kuma ana sa ran zai bayyana majalisar zartarwarsa a yau Talata kamar yadda wasu mijiyoyi biyu na gwamnatin suka bayyana wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

Majiyoyin da basu so a bayyanasu ba, saboda a cewarsu ba a basu ikon magana ba da manema labarai ba, Majuru ta karbi takardar sallamarta a daren jiya Litinin makonni bayan da ake zirginta da kitsa wani shiri na kawar da gwamnatin ta shugaba Mugabe.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu