Mugabe ya kare nasarar jami'yyarsa
August 12, 2013Daɗaɗɗen shugaban ƙasar Zimbabwe Robert Mugabe ya ce babu yadda za a yi jamiyyarsa ta miƙa wuya ga duk wani yunƙuri na sauya nasarar da ta yi a zaɓukan ƙasar ba, inda ya ce duk da cewa ana ƙalubalantan sakamakon, masu sanya ido daga ƙasashen Afirka sun amince da shi, kuma sun ce zaɓe ne da aka gudanar ba tare da tashin hankali makamancin wanda ya afku a shekarun baya ba.
A jawabinsa na farko cikin bainar jama'a, tun bayan zaɓen na 31 ga watan Yuli, Mugabe ya tattauna batun zaɓen yayin taron shekara-shekara na tunawa da dakarun da suka rasu lokacin yaƙin neman 'yancin kan ƙasar a shekarar 1980.
Mai shekaru 89 ya haƙiƙance kan cewa al'umma ce ta zaɓe shi da san ranta ba tare da an tilasta mata ba. Babban abokin hammayarsa Morgan Tsvangirai wanda ke ƙalubalantar sakamakon a Kotu wanda kuma zargin an yi maguɗi a kowani mataki na zaɓen ya ƙauracewa wannan taron karrama tsoffin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya, duk da mahimmancinsa ga tarihin ƙasar.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe