Mubarak zai sake gurfana a gaban kuliya | Labarai | DW | 24.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mubarak zai sake gurfana a gaban kuliya

Tsohon shugaban Masar zai fuskanci zargin haddasa mutuwar masu zanga-zanga lokacin juyin-juya hali.Yayin 'yan 'Yan Uwa Musulmi kuwa za a tuhumesu da tayar da zaune tsaye.

Tsohon shugaban kama karyar Masar Hosni Mubarak zai koma kotu ranar lahadi inda zai fuskanci zargin da ake masa na cewa shi ke da alhakin mutuwar ɗaruruwar masu zanga-zanga a lokacin kaɗawar guguwar juyin-juya halin da ta kifar da gwamnatinsa a shekarar 2011. A yayin da a shari guda kuma jagororin ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi biyu, su ma zasu bayyana a gaban kotu a karo na farko dan fuskantar zargin da ake musu na harzuƙa 'yan ƙasa da haddasa tashe-tashen hankula .

Shari'o'in biyu da za a gudanar a babban birnin ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da tashe-tashen hankula ke ta'azara a sanadiyyar rikicin siyasar da ya tirnaƙe a ƙasar tun bayan hamɓarar da shugaba Mohammed Mursi ranar uku ga watan Yuli. Kamfanin dillancin labarun AFP ya rawaito cewa mahukuntan Masar sun ba da sammacin kama ɗaruruwan mambobin ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmin kuma wata majiyar tsaro mai tushe ta ce aƙalla magoya bayan jam'iyyan dubu biyu ne ke tsare.

Duk da rashin daidaito da ci-gaban da zaman fargaban da 'yan ƙasa ke yi gwamnatin ta haƙiƙance cewa za ta ci-gaba da aiwatar da taswirar hanyar da ta zana wadda ta tanadi samar da sabon kundin tsarin mulki da gudanar da zaɓe; matakan da ƙungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta ce ba za ta amince da su ba.

Mawallafiya: Piando Abdu Waba

Edita: Mouhamadou Awal Balarabe