1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mozambik:Afonso Dhlakama ya rasu

Abdourahamane Hassane
May 3, 2018

Shugaban jami'yyar 'yan adawa na Mozambik kana tsohon dan tawaye na RENAMO Afonso Dhlakama, ya rasu a sakamakon fama da ya yi da ciwon bugon zuciya.

https://p.dw.com/p/2x8OE
Afonso Dhlakama
Afonso Dhlakama jagoran 'yan adawa na MozambikHoto: picture-alliance/dpa/A. Silva

Afonso Dhlakama dan shekaru 65 wanda ya jagoranci RENAMO sama da shekaru 30 yana yakar gwamnatin FRELOMO kafin daga baya RENAMO ta rikide ta koma jam'iyyar siyasa bayan kawo karshen yakin basasar kasar a shekara ta 1992. Za a jima ana tunawa da shi, saboda irin gudunmowar da ya ba da don samar da zaman lafiya a kasar Mozambik.