1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'aa na ficewa daga Cabo Delgado saboda 'yan ta'adda

Abdourahamane Hassane
February 27, 2024

Gwamnatin Mozambik ta tabbatar da cewar dubun dubatar mutane ne, suka ficce daga matsugunansu sakamakon hare-haren masu jihadi na baya-bayan nan a arewacin kasar,.

https://p.dw.com/p/4cxRf
Hoto: Delfim Anacleto

Sama da mutane dubu   67suka rasa matsugunansu in ji mai magana da yawun gwamnati Filimao Suaze a wani taron manema labarai da ya yi a  birnin Maputo,yayin da yake magana kan halin da ake ciki a lardin Cabo Delgado. Kusan mutane dubu biyar ne aka kashe yayin da wasu miliyan guda suka rasa muhallansu tun farkon rikicin a yankin na Cabo Delgado inda masu jihadi ke kai hare-hare.