1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mozambik: Juyayin rasuwar jagoran RENAMO

Mohammad Nasiru Awal SB
May 4, 2018

Afonso Dhlakama da ke zaman dadadden jagoran kungiyar RENAMO ta 'yan tawayen kasar Mozambik wanda kuma ya kasance shugaban jam'iyyar adawa a kasar, ya rasu yana da shekaru 65 a duniya. 

https://p.dw.com/p/2xBtw
Mozambique Government Renamo peace agreement
Marigayi Afonso Dhlakama shugaban jam'iyyar adawa ta RENAMO a Mozambik lokacin tattaunawar zaman lafiyaHoto: picture-alliance/dpa/A. Silva

Rasuwar ta Dhlakama da ta a zo a cikinn yanayi na ba zata, ta sanya shakku kan shirye-shiryen da ake na samar da zaman lafiya a kasar. Mutuwar ta zo ne a daidai lokacin da kungiyarsa ta RENAMO ke tattauna batun zaman lafiya da gwamnati dangane da raba ayyukan hukumomin gwamnati da kuma kwance damaran mayaka. Saboda haka manazarta ke kallon mutuwar a matsayin tsaiko ga tattaunawar samar da zaman lafiya. Silvestre Baessa masani ne kan samar da kyakkyawan shugabanci a kasar ta Mozambik wanda ya ce yanzu an shiga wani yanayi na rashin sanin tabbas sakamakon mutuwar jagoran 'yan adawar:

Afonso Dhlakama
Afonso Dhlakama a birnin Maputo a watan Satumba na 2014Hoto: picture-alliance/dpa/A. Silva

"Mutuwar Dhlakama za ta yin tasiri a fagen siyasar kasar. Da farko dai mun yi rashin babban jagora a tattaunawar samar da zaman lafiya. A shekarun baya ya bayyana afili cewa shugaban na RENAMO ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin an samu zaman lafiya a Mozambik. Rashinsa na zama babban kalubale ga shirye-shiryen samar da zama lafiyan. Shugaban kasa Filipe Nyusi zai ji zafin wannan rashi domin Dhlakama ya kasance babban abokin tattauawarsa a shirin na zaman lafiya a cikin jam'iyya da kuma kasa baki daya."

Dhlakama wanda ya rasu a ranar Alhamis sakamakon ciwon bugun zuciya, ya kwashe shekaru 39 yana jagorantar kungiyar 'yan tawaye ta RENAMO wadda ta kwashe shekara 16 tana yakar jam'iyyar FRELIMO da ke mulki har zuwa karshen yakin basasa a shekarar 1992. Yakin daya ne daga cikin mafiya muni a Afirka da ya yi sanadin rasa rayukan mutane kimanin miliyan daya sannan wasu miliyoyi suka rasa muhallansu. 

Mosambik  Afonso Dhlakama
Afonso Dhlakama lokacin yakin neman zaben shugaban kasa a 2014Hoto: Getty Images/S. Costa

A karshen yakin kungiyar tawayen ta RENAMO ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa a matsayin mai adawa, amma ta ci gaba da rike bangaren mayakanta. Dhlakama ya yi takarar neman shugabancin kasar amma ba yi nasara ba. A watan Nuwamban 2015 rikice ya sake barkewa, kusan shekaru biyu bayan da Dhlakama da na hannun damarsa sun boya a yankin tsaunuka na kasar. A watan Disamban 2016 ya ayyana yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati.

A wannan Jumma'a ce shugaban kasa Felipe Nyusi ya ce bai kamata kwarya-kwaryar shirin zaman lafiyar kasar ya ruguje sakamakon mutuwar jagoran 'yan tawayen ba. To wai shin me yasa shugaba Nyusi ya nuna damuwa dangane 
da shirin zaman lafiyar bayan mutuwar Dhlakama?  Alex Vines shugaban sashen nazarin harkokin Afirka a cibiyar nazarain harkokin siyasar duniya ta Chatham House da ke birnin London, ya yi karin haske:

"Ana dab da kammala shirin zaman lafiya da aka faro tun a watan Disamban 2016, ana cikin lokaci mafi dacewa na cimma wata yarjejeniya. Mutuwarsa na zama babban hatsari ga shirin kasancewa shi ke wakiltar kungiyar RENAMO a shirin kuma bai wakilta wani a madadinsa ba."

Mutuwar Dhlakama dai ta tayar da tambaya game da makomar kungiyarsa da ya jagoranta kusan shekatru 40. Ba a kuma san wanda zai ci gaba da tattaunawa da gwamnatin ba.