Moussa Ibrahim ya ce ba a kama shi | Labarai | DW | 21.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Moussa Ibrahim ya ce ba a kama shi

Kakakin tsohon shugaban Libya Moammar Gadhafi, Moussa Ibrahim ya musanta iƙirarin kama shi da mahukuntan Libya su ka yi kusa da birnin Trabulus, fadar gtwamnatin ƙasar.

A wani sako na murya da ya sanya a shafin internet na Youtube, Moussa Ibrahim ya ce ko kusa baya hannun mahukuntan na Libya kamar yadda su ka yi iƙirari hasalima ba ya ƙasar baki ɗaya.

Tsohon kakakin na gwamnatin Ghaddafi ya ce bada labarin kama shi wani yunƙuri ne da gwamnatin ƙasar ke yi na kawar da hankalin al'ummar ƙasar daga irin cin zarafin da ake yi wa mutanen da ke garin Bani Walid wanda ke zaman yanki na ƙarshe da aka karɓe kafin faɗuwar gwamnatin Ghaddafi.

Wannan saƙo na sautin Moussa Ibrahim wanda ba a tanatance sahihancinsa ba dai na zuwa ne daidai lokacin da mahukuntan ƙasar ta Libya su ka yi shelar kama shi a garin Tarhouna, shekara guda kenan bayan da aka hambarar da gwamnatin shugaba Ghaddafi bayan da ta shafe shekaru sama da arba'in a kan gadon mulki.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Umaru Aliyu