1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Man U ta kori Mourinho

Gazali Abdou Tasawa
December 18, 2018

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasar Birtaniya, ta kori mai horas da 'yan wasanta Jose Mourinho a wannan Talata shekaru biyu da rabi bayan soma aiki da kungiyar.

https://p.dw.com/p/3AJrt
Fußball Mimik Trainer Jose Mourinho
Hoto: picture-alliance/Offside/M. Atkins

Rahotanni daga Birtaniya na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami mai horas da 'yan wasanta Jose Mourinho. Kungiyar ta Man United wacce ke zama kungiyar kwallon kafa mafi karfin tattalin arziki daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na duniya, ta dauki wannan mataki bayan kashin da ta sha a gaban Liverpool a karshe mako a wasannin Premier League, inda a yanzu ta koma a matsayin ta shida a tebirin na Premier League. 

Mourinho dan asalin kasar Potugal mai shekaru 55 a duniya wanda ya horas da manyan kungiyin kwallon kafa na Turai irinsu Real Madrid da Inter Milan da Chelsea ya lashe kofin zakarun Turai sau biyu a lokocin da tauraronsa ke haskawa, zai bari kungiyar ta Man United wacce ya share shekaru byu da rabi yana horas da 'yan wasanta, inda ya yi nasarar lashe gasar League Cup da kuma Europa League. 

To sai dai a shekarun baya-bayan nan kukuwarsa ta daina ci inda a yanzu ya fi mayar da hankali ga rikici da 'yan wasansa kamar yadda ta ksance a tsakaninsa da Paul Pogba shahararren dan wasan da kungiyar ta Man U ta sayo da tsada, da amma ke gugar bencin kungiyar a sakamakon sabaninsa da kociyan nasa. A yanzu dai Kungiyar ta ce za ta nada wani sabon mai horas da 'yan wasa na wucin gadi da zai jagoranci kungiyar har zuwa karshen kakar wasannin shekarar bana.