1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko ta yi barazanar zuwa kotu

Abdoulaye Mamane Amadou
July 22, 2021

Gwamnatin Moroko ta yi barazanar shigar da karar duk wata kasar da ke ci gaba da yi mata kage kan amfani da manhajar Pegasus don lekon asirin wayoyin jama'a.

https://p.dw.com/p/3xokM
Israel | NSO Group
Hoto: Jack Guez/AFP/Getty Iamges

A tsakiyar wannan makon ne dai wani rukunin masu bincike suka bankado cewa an yi amfani da manhaja mallakar wani kamfani mai suna NSO na Isra'ila, wajen sauraren wayoyin dumbin jama'a da suka hada da 'yan siyasa da 'yan jarida da masu fafatukar kare hakkin bil Adama da ma wasu jami'an gwamnati ciki har da Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Gwamnatin Morokon dai ta karyata wannan batun tana mai cewar za ta gudanar da bincike a kai.