1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moritaniya: El Ghazouani ya lashe zabe

Gazali Abdou Tasawa
June 23, 2019

A kasar Moritaniya, dan takarar jam'iyya mai mulki a zaben shugaban kasa da ya gudana a jiya Asabar Mohamed Cheikh El-Ghazouani ya lashe zaben tun a zagayen farko da kashi 51,1% na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/3KwE9
Mauretanien |  Präsidentschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

El Ghazouani ya samu kashi 51,1% na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Moriteniya a cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta wannan kasa. Dama dan takarar ya bayyana lashe zaben ne a cikin daren jiya Asabar zuwa wannan Lahadi a gaban tarin magoya bayansa da ma Shugaba mai ci Mohamed Ould Abdel Aziz, a daidai lokacin da hukumar zaben ke ci gaba da kidaya kuri'un. 

Wata majiya daga hukumar zaben kasar ta bayyana cewa El Ghazouani dan takarar jam'iyya mai mulki ya samu kaso 50,56 cikin dari tun a lokacin da aka kidaya kaso 80 daga cikin dari na kuri'un da aka kada, a yayin da manyan abokan hamayyarsa Sidi Mohamed Ould Boubacar da Biram Ould Dah Abeid kowannensu ya samu kaso 18 cikin dari. 

Ya zuwa yanzu dai ba daya daga cikin 'yan takara biyar da suka fafata da El-Ghazouani da ya fito ya ce wani abu kan wannan sanarwa. Sai dai tun a jiya Asabar hudu daga cikinsu sun yi zargin tafka magudi a zaben da ma korar wakillansu daga runfunan zabe.