1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar tsaron Jamus tana arewacin Mali

Suleiman BabayoApril 5, 2016

Yayin ziyarar ministar tsaron ta Jamus Ursula von der Leyen za ta gane wa idonta aikin da dakarun kasar ke yi karkashin Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/1IPbs
Ursula von der Leyen in Mali Tieman Hubert Coulibaly
Hoto: Reuters/M.Kappeler

Ministar tsaron kasar Jamus Ursula Von der Leyen ta isa garin Gao na arewacin Mali, inda akwai fiye da sojojin Jamus 200 wadanda suke karkashin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. Kimanin watani biyu da suka gabata dakarun Jamus suka fara isa kasar ta Mali kuma zuwa watan Yuni za a nunka yawan sojojin.

Jamus ta kasance daya daga cikin masu tallafawa domin samar da zaman lafiya a Mali tun lokacin da kasar ta shiga cikin rudani a shekara ta 2012, abin da kai ga sojojin Faransa suka yi amfani da karfin wajen sake kwato yankunan da tsageru masu kaifin kishin addinin Islama suka kwace daga hannun dakarun gwamnati.