Ministan makamashin Benin ya yi murabus | Labarai | DW | 13.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministan makamashin Benin ya yi murabus

Badakalar zargi na sama da fadi da dukiyar kasa ta yi awon gaba da kujerar minista Barthélémy Dahoga a gwamnati Boni Yayi ta jamhuriyar Benin

Ministan makamashin da albarkatun ruwa na kasar Benin Barthélémy Dahoga ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon wata badakalar cin hanci da karbar da rashawa da ake zarginsa da aikatawa. Wani bincike da aka gudanar ya nunar da cewar miliyan hudu na Euro sun bace a ma'aikatarsa daga kudin da kasar Holland ta bayar don wadata al'umma da ruwa mai tsafta, lamarin da ya sa Holland din dakatar da tallafin da ta saba bayarwa.

Gwamnatin ta Benin ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan badakalar kudin tsakanin manyan jami'an ma'aikatar ta makamashi da albarkatun ruwa. Da ma dai tun bayan da ya dare kan karagar mulki shekaru taran da suka gabata, Shugaba Boni Yayi ya yi alkawarin yakar almundahana da dukiyar kasa. Sai dai kuma gwamnatinsa ta ci karo da badakalar cin hanci ciki kuwa har da karkata akalar kudin gina sabuwar majalisar dokoki a kasar.