1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Minista tayi murabus kan rashin hukunta masu fyade

Ramatu Garba Baba
September 27, 2021

Ministar ma'aikatar mata a Habasha ta sanar da yin murabus bayan da aka gagara hukunta wadanda aka gano sun aikata laifukan fyade da cin zarafin mata a yankin Tigray.

https://p.dw.com/p/40wuo
Äthiopische Tigray-Migranten
Hoto: picture-alliance/AP Images/N. El-Mofty

Ministar ma'aikatar mata a Habasha da ta fito fili ta amince da labarin aikata laifuka na fyade a yankin Tigray, ta sanar da yin murabus daga mukaminta a wannan Litinin. Filsan Abdullahi Ahmed ba ta fadi dalilinta na yin murabus ba, sai dai kawai ta ce, ba za ta laminci duk wani aiki da zai keta mutunci da kuma sabawa 'yancinta dana sauran 'yan kasa ba. Ta fadi hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter.

A watan Febrairun da ya gabata ne, Miss Filsan ta kaddamar da wani kwamitin da aka dorawa aikin binciken zarge-zargen yi wa mata fyade a tsawon watanni 10 da aka kwashe ana fada a tsakanin rundunar gwamnatin Habashan da 'yan tawayen TLP na Tigray, sakamakon binciken, ya tabbatar da zarge-zargen wanda ya sa, ta nemi a dauki matakin hukunta wadanda keda hannu a aika-aikan.

Ba a dai kai ga daukar matakin ba ya zuwa yanzu. Dama Kungiyar Amnesty International  a wani rahoto da ta fitar a watan jiya, ta ce, rundunar sojin Habasha dana Iritirya sun yi wa daruruwan mata da ke yankin Tigray fyade baya ga gallaza musu azaba.