1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin yara na fuskantar barazanar kamuwa da cutar kyanda

Binta Aliyu Zurmi
November 24, 2022

A sanarwar hadin gwiwa da suka fitar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO da cibiyar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a kasar Amirka, sun ce an sami koma baya a rigakafin cutar kyanda.

https://p.dw.com/p/4JywV
14. Weltgesundheitsgipfel | Tedros Adhanom Ghebreyesus
Hoto: Carsten Koall/dpa/picture alliance

A rahotonsu na jiya Laraba, sanarwar ta kara da cewar sama da yara miliyan 40 ne basu cikashe rigakafinsu ba a shekarar da ta gabata, bisa tafiyar hawainiya da rigakafin ke fuskanta tun bayan bullar cutar corona a duniya.

Yanzu haka dai hukumar ta WHO ta ce miliyoyin yara ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar, a shekarar 2021 sama da yara miliyan 9 ne cutar ta kamasu yayin da ta yi sanadiyyar rayukan kusan dubu 130 a fadin duniya.

Masana kimiya sun ce akwai bukatar yin rigakafi ga akalla kaso 95 cikin dari na al'umma da cutar ke wa barazana a wani mataki na dakile yaduwar ta da ke bazuwa tsakanin mu'amalar mutum da mutum ko ma a shaka ta iska.

Mafi akasari cutar kyanda ta fi yin illa ga yara a nahiyar Afirka da kuma kasashen yankin Asiya.