1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mike Pompeo na ziyara a Isra'ila

August 24, 2020

Sakataran harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya fara wani rangadi a yankin Gabas ta Tsakiya domin shawo kan kasashen yankin su amince su daidaita huldar su da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/3hR0J
Israel | PK US-Außenminister Mike Pompeo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/D. Hill

Mike Pompeo wanda ya soma da Isra'ila ya gana da firaminista Benyamen Netanyahu kafin ya isa a Baharain  da Jordan da Sudan wacce tuni ta sake daidaita hulda da Isra'ilan wadda Pompeo zai je ya jinjina wa kasar: Yarjejeniyar da aka cimma a cikin watan Janairu da ya gabata  tsakanin Amirka da Hadadiyar Daular Larabawa  ta tanadi cewar Isra'ila ta kawo karshen mamaye yankunan Larabawa don tabbatar da zaman lafiya.