Michel Djotodia zai fuskanci hukunci | Labarai | DW | 26.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Michel Djotodia zai fuskanci hukunci

Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci da a hukunta tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Michel Djotodia.

Kwamitin sulhu na Majaliar Ɗnkin Duniya ya buƙaci da a hukunta tsohon shugaban ƙasar, saboda abin da ya kira hana ruwa gudu a mulkin gwamnatin riƙon ƙwarya da ya jagoranta.

Michel Djotodia shi ne ke kan gaba a cikin wasu jerin sunaye guda 15 wanda majaliar ta gabatar,waɗanda suka haɗa da sojoji da farar hula waɗanda ake zargi da hannu wajen kawo tarnaƙi ga shirin wanzar da zaman lafiya a ƙasar.Hukuncin da Majalsar ta Ɗinkin Duniya ta tattauna a kansa tun cikin watan Janairun da ya gabata, ya haɗa da soke kuɗaɗen ajiya na mutanen a bankuna da kuma haramta musu yin tafiye-tafiye.