MH370: Malesiya na binciken tarkacen wani Jirgi | Labarai | DW | 22.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MH370: Malesiya na binciken tarkacen wani Jirgi

Hukumomin Malesiya na shirin aikewa da wata tawaga ta kwararru domin tantance tarkacen wani jirgi da aka gano a kudancin gabar ruwan Afirka ta Kudu ko yana da alaka da jirgin kasar mai suna MH370.

Tarkacen jirgin dai an gano shi ne a garin Mosselbay a ranar Talatar nan kuma masanan na cewar mai yi wa ne yana da alaka da jirgin saman Malesiya nan da ya bace yau kimanin shekaru biyu da suka gabata.

Humkumomin kasar Malesiya suka ce za su kara gudanar da bincike a kan tarkacen jirgin kafin a gane ko yana da alaka da MH370 ko akasin haka.

Shi dai jirgin saman Malesiya kirar MH370 wanda yake dauke da fasinjoji 239 da matukan sa sun bace ne jim kadan da tashin su daga filin jirgin saman Kuala Lumpur domin tinkarar birnin Beiging kimanin shekaru biyu ke nan.