1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Messi zai taka leda a Katar

Abdul-raheem Hassan
November 21, 2022

Keptin din tawagar 'yan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Lionel Messi, ya ce ya shirya taka leda a gasar cin kofin duniya na 2022 a Katar wanda shi ne karonsa na biyar kuma kila na karshe.

https://p.dw.com/p/4JqD0
Lionel Messi
Hoto: Eduardo Munoz Alvarez/AP Photo/picture alliance

Dan wasan Messi mai shekaru 35 a duniya, ya yi rashin nasara sau uku a karawarsu da Jamus a shekarar 2006 da 2010 a wasan daf da na kusa da na karshe da kuma wasan karshe a 2014, kuma a shekarar 2018 an fitar da su a zagaye na 16 na karshe a karawarsu da Faransa mai rike da kofin.

Amma haryanzu Messi ya ce bai cire tsammanin daga kofin ba a gasar bana da ake fafatawa a Katar, Ajantina za ta yi karawar farko da Saudiyya.