MEND ta yi barazanar tada kayar baya | Siyasa | DW | 15.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MEND ta yi barazanar tada kayar baya

Matakin kai hare-hare da kungiyar gwagwarmayar kwatar 'yancin Niger Delta ke shirin dauka ka iya kara tabarbarra da tsaro a Najeriya da kuma kawo cikas ga aiyukan hakar man fetur.

Tun dai bayan ikirarin da babbar kungiyar 'yan bindugar yankin Niger-Delta,wato MEND ta yi kan cewar za ta fara kai munanan hare-hare a yankin, da ma wasu sassan Najeriya,da alamu wannan barazana ka iya sauya yadda yanayin yankin yake,musamman ma game da harkokin aiyukan fidda mai.

Wannan barazana dai ta wani bangaren kungiyar ta MEND da dama bai na'am da shirin afuwar gwamnatin Tarayyar Najeriya ba,cewar za ta fara kai hare-hare da suka hada da kan harkokin mai a yankin Niger-Delta,barazana ce da ga dukkanin alamu ta fara jan hankulan kamfanoni mai a yankin.

Kungiyar dai ta jima ba aji duriyarta ba,in banda a bayan nan da tai wannan furuci na juyowa da kai hare-hare.

Ko da yake kamfanonin mai da dama sun ki cewar uffan kawo lokacin hada wannan rahoto, kan wannan barazana da ire-iren ta su kai tasiri a baya,sai dai akwai wani jami'in kamfanin man Agip da bai san ambatar sunansa ,da ya tabbatar min cewar hakan ba zai sauya salon yadda suke aiyukan u na mai ba a cikin surkukin yankin na Niger-Delta,sai dai kawai yanzu sun daina yawan tafiye- tafiye ta jiragen ruwa face fa jirage ma su saukar angulu a yankin.Shi kuwa kakakin kamfanin shell cewa yayi gwamnatin tarayya ita ke da alhakin ta cewa game da tsaro,dan haka ba shi da ta cewa kan hakan.Sai dai kuma da dama wayan da ke aiyukan na mai da naji ta bakinsu, sun baiyanar cewar wannan barazana ta MEND abin ayi hattara ne kuma abin damuwa.

Wannan wani dan jarida ne a Ndelta da kuma bai san fadin sunansa,mai kuma bin diddigin abin da ke faruwa a yankin.

Rundunar gamayyar tsaro ta JTF da ke aikin tsaro a harabobin ayyukan mai a yankin na Niger Delta ta shaida min ta waya ta bakin kakakinta Litana Kalan Etete cewar su kam a shirye suke a koda yaushe kan dukkanin kalubale da ka iya fuskantar yankin da suke aiki,dan haka ikirarin na MEND in har gaske ne,to ba wani abu bane sabo gare su.

Wani dattijo ,Mr Jesus Doukoru da ke zaman dan yankin na Niger- Delta da yayi tsokaci ransa a bace cewa yayi:

Logo von Royal Dutch Shell, Öl Firma, und Nigeria (Rebellen in Niger Delta)

Yayin da Amurka ta furta a baya cewar Najeriya ta kama hanyar jagorancin kasashe da ke da 'yan ta'adda musawa mu ka yi ,amma kuma gashi yanzu halin da muke ciki na ta'addanci ya kazanta,makamai ko ina,har yanzu kuma akwai manya manyan makamai da aka gaza karba daga hannun 'yan bunduga, da 'yan siyasa sune ummul abaisun duk wannan masifa.

Gararin hare-haren 'yan bindugar MEND dai,wadda kungiya ce da ta hada kungiyoyin 'yan binduga da dama a yankin na Niger Delta,ta yi yayin kai hare-hare munana a baya a kan kamfanonin aiyukan mai da jami'ansu,wadda kuma ya haifar da matikar koma baya a harkokin man Najeriya.

Wasu dai dubban 'yan bindugar da har yanzu ke ta fafutukar shiga shirin afuwar gwamnati,ba kuma tare da samun nasara ba,ma su lura na hangen,ka iya shiga shirgin na kungiyar ta MEND.

Mawallafi: Mohammed Bello
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin