Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi martani a kan sabuwar gwamnatin Amirka da Shugaba Joe Biden ke jagoranta, da yadda ake ganin dangantakarsa za ta kasance da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Akwai kuma kokari da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ke yi a Najeriya na kawo karshen rashin zaman lafiya.
Kwararru a harkokin lafiya a Najeriya na nuna damuwa kan yadda jama'a da dama basa bada hadin kai kan yadda ake kokarin shawo kan annobar Corona a kasar musamman yadda jama'a ke kin zuwa a auna su.
A cikin shirin za ku ji cewa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta bukaci a yi adalci wajen rarraba alluran rigakafin annobar coronavirus. Akwai sauran labarai da kuma shirinmu na Afirka a mako, dake waiwaye kan muhimman al'amuran da suka faru a nahiyarmu ta Afirka a mako mai karewa.
Wata cuta da ke damun mata masu shekaru na karkara Agadez da ke Jamhuriyar Nijar ita ce cutar fitsari.
A birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar, hadakar kungiyoyin addinai sun bayar da horo ga sarakunan gargajiya da malamai da kuma mata dangane da kyautata zamantakewa a tsakanin al'umma domin a samun zaman lafiya. Ku saurari shirin Taba Ka Lashe.
A Jamhuriyar Nijar huldar da tashar DW ta kulla tare da wasu gidajen radiyoyi masu zaman kan, na taka babbar rawa wajen bai wa al’ummar kasar damar samun labarai da shirye-shiryen na DW cikin sauki ba tare da sun sha wahalar neman tashar ba.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a Jamhuriyar Nijar, ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi.
Shirin ya yi nazari kan yadda mutane kan jibge tsoffin karafa, ko kayyayakin da aka gama amfani dasu a wuraren da jama’a ke rayuwa ba tare da la’akari da illolin dake akwai ga lafiyar jama'a ba.
A kowace shekara sarar maciji fiye da dubu 25 ne ake samu a lokacin shara da kuma girbin amafanin gona a Tarayyar Najeriya.
A Jamhuriyar Nijar a yayin ake shiga manyan zabukan kasar shugabannin hukumar sadarwar kasar CSC sun da hanyoyin yakin neman zabe a kafofin yada labarai na gwamnati da masu zaman kansu.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a rage takurar da ake yi kan ganyen wiwi saboda ana iya amfani da shi ta hanyar magani.
Wasu iyaye da dama, ba sa son shayar da jariransu nono uwa. Shin ko me yake janyo hakan? Shirin Lafiya Jari ya ji ta bakin wasu mata, da ma illolin hakan ga lafiyar uwa da jariri.
Bayan labaran duniya da rahotanni za a ji cewa, a wannan Alhamis shugabanin kasashen duniya kimanin 100 ke soma zaman taron kwanaki biyu na Majalisar Dinkin Duniya domin lalubo dabarun kawar da annobar corona daga doron kasa.
A yayin da ake kokarin kai mataki na karshe na amincewa da allurar rigakafin corovirus, masana kiwon lafiya na gargadin al'umma cigaba da matakan kariya.
A cikin shirin za a ji a jamhuriyyar Nijar a daidai lokacin da aka soma zaman makoki na kwanaki uku, bangarori dabam-daban na tuna muhimman ayyuka na ci gaba da tsohon Shugaban kasar Mamadou Tandja ya yi wa kasar.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoton kan kaddamar da matatar man fetur ta farko mai zaman kanta da aka yi a Najeriya da rahoto kan yadda ake zargin 'yan siyasar Nijar da rasa alkibla a daidai lokacin da zaben shugaban kasar ke kara karatowa. Muna kuma dauke da halin da ake ciki dangane zaben shugaban kasa na Burkina Faso da kuma halin tsaro a yankin Tigray na Habasha.
Rikicin 'yan aware na kara fadada a nahiyar Afirka. Na baya-bayan nan da ke ci gaba da ta'azzara, shi ne na 'yan awaren Tigray da ke kasar Habasha. Wannan na zaman misali ne kawai.
A cikin shirin za a ji labarin duniya da rahotanni ciki har da sanarwar Hukumar Lafiya ta Duniya da ta baiyana farin ciki bayan tabbacin ingancin allurar riga-kafin cutar corona daga kamfanin magani na AstraZeneca. Ana fatan ganin riga-kafin zai kai ga kowa.
Jakadan musamman na hukumar kula da lafiya ta MDD kan COVID 19 David Nabarro, ya yi hasashen yiwuwar barkewar annobar corona a karo na uku a Turai, a farkon shekara ta 2021 kafin fara allurar riga kafin wannan muguwar cuta.
Ko kun san dalilan da ke haddasa cutar dimuwa ko kuma mantuwa? Shin masu yawan shekaru ne kadai ke fama da wannan cuta ko kuwa masu kananan shekaru ma na tsintar klansu cikin wannan lalura? Shirin Lafiya Jari.