Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi martani a kan sabuwar gwamnatin Amirka da Shugaba Joe Biden ke jagoranta, da yadda ake ganin dangantakarsa za ta kasance da kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Akwai kuma kokari da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ke yi a Najeriya na kawo karshen rashin zaman lafiya.
A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji yadda Shugaba Joe Biden na Amirka ya sha rantsuwar kama aiki. Muna dauke da rahoto game da martanin da ’yan Najeriya da Nijar da sauran kasashen Afirka ke yi game da kama aikin da Joe Biden ya yi.
Sana'o'in dpgaro da kai na da matukar muhimmanci a tsakanin al'umma musamman ma matasa. Yanzu a nahiyar Afirka, matasan kan rungumi sana'o'in domin su dogara da kansu.
Kwararru a harkokin lafiya a Najeriya na nuna damuwa kan yadda jama'a da dama basa bada hadin kai kan yadda ake kokarin shawo kan annobar Corona a kasar musamman yadda jama'a ke kin zuwa a auna su.
Ko kun san hanyoyin da za a bi wajen hada kan mabiya mabanbamtan addinai a Najeriya? Shirin Taba Ka Lashe ya yi nazari kan wannan batu.
Doya na daga cikin kayan abincin da aka fi hada-hadarsu a jihar Kano da ke Najeriya, duk da cewa ba a noma ta a Kanon. Wani bangare na kasuwar Dawanau da ake kira Rami na hada hadar doyar da ake kawowa daga jihohin da suka shahara wajen nomanta. Daga nan ne ake hada hadar ta zuwa sauran garuruwa da ma wasu kasashe.
Usman Muhammad wani matashi ne a jihar Gombe da ke Najeriya, wanda bayan ya kamala karatunsa ya rungumi sana'ar yankan farce wacce ake ganin kamar ba sanar wadanda su ka yi karatun zamani ba ce.
Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Airka ta Tsakiya ta tabbatar da zaben da Shugaba Faustin Archange Touadera ya lashe na watan jiya na Disamba, amma ta ce tashin tankali na kungiyoyi masu dauke da makamai ya dakile fitowar masu kada kuri'a.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan kaurace wa garin Marte da jama’a ke yi bayan da harin da Boko Haram ta kai a karshen mako sannan muna dauke da rahoto kan bude makarantu a jihar Filato Najeriya da rahoto kan samun wasu jami’ai da hannu a safarar hodar iblis a Nijar.
A cikin shirin za a ji cewa dakarun tsaron Najeriya sun kwace iko da barikin sojan garin Marte da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya, a yayin da sojan Munisca naMajalisar dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka karbe iko da garin Bagassou daga hannun 'yan tawaye.
A cikin shirin za aji cewa a karo na shida a cikin shekaru 35 shugaban Yuganda ya lashe zaben shugaban kasa, a Najeriya kuwa an kammala zabukan kananan hukumomin jihar Kano 44 wanda jamiyyar APC mai mulki ta lashe zaben.
A cikin shirin za a ji cewa Bayan fafatawa tsakanin 'yan takara, gwamnan jihar NRW Armin Laschet, ya yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyar CDU. Akwai shirin ciniki da masana'antu da amsosshin takardunku da shirin wasikun masu saurare da kuma Kloba.
A cikin shirin za a ji cewa an kaddamar da allurar rigakafin kamuwa da cutar corona a kasar Indiya, a yayin da a kasar Jamus ake dakon zaben sabon shugaban jam'iyyar CDU mai mulki don maye gurbin Angela Merke da ke shirin bankwana da mulki. Akwai Afirka a Mako da ke bibiyar muhimman batutuwan da suka ja hankali a Afirka.
Gwamnatin tarayar Najeriya ta sanar da karin bude wasu iyakokin ta da sauran kasashe makobta wanda aka kwashe sama da shekara daya suna rufe. Hakan ya janyo martanin daga bangarori dabam-dabam a Nijar da Najeriya.
A cikin shirin za a ji a Najeriya hukumar rijistar dan kasa ta bullo da wata manhaja da za’a iya sada lambobin waya da lambar zama dan kasa domin rage wahalhalu da cunkoson da ake fuskanta wajen wannan aiki.
A cikin shirin bayan rahotanni za ku ji cewa mayakan yankin Ingilishin Kamaru sun yi barazanar gurgunta harkokin wasannin kwallon kafa. Muna dauke da rahoto kan amfani da sabuwar fasahar Jamus ta adana amfanin gona da Najeriya ta fara amfani da ita. Akwai rahoto kan darasin da corona ta koya wa jama’ar Nijar a lokacin zaben shugaban kasar da ya gabata.
Shirin ya kunshi labaran duniya da kuma halin da ake ciki na yajin aiki da likitoci suka fara a Nijar. A Najeriya masarautar Argungu da ke jihar Kebbi ta sasanta rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma. Abzinawan kasar Aljeriya kuma biki suka yi na shiga sabuwar shekarar gargajiya.
A Jihar Taraba da ke a arewacin Najeriya matasa sun rugumi sana'ar wanki da guga, domin samun abin dogaro da kai. Wannan shi ne batun da shirin Dandalin matasa ya duba.
A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan halin da ake ciki a Amirka bayan majalisar wakilan kasar ta tsige Donald Trump da rahoto kan gasar rubutun wakokin Hausa da aka fito da ita a Najeriya da zummar magance matsalar tsaro da kuma rahoto kan bikin sabuwar shekarar Abzinawa a Aljeriya.
Za a ji yadda ake fa,ma da cunkoso a Najeriya a wuraren da ake rajistar dan kasa daidai kuma lokacin da annobar corona ke kara yaduwa. A Nijar kuma kananan jam'iyyu ne suka hada karfi don tinkarar dan takara a jam'iyya mai mulki a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.