Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi labaran duniya da kuma halin da ake ciki na yajin aiki da likitoci suka fara a Nijar. A Najeriya masarautar Argungu da ke jihar Kebbi ta sasanta rikici tsakanin makiyaya da kuma manoma. Abzinawan kasar Aljeriya kuma biki suka yi na shiga sabuwar shekarar gargajiya.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya kuncin rayuwa ya ragewa bikin kirismetin bana armashi a kasar a yayin da a Chadi al-ummar kasar ne ke kira ga gwamnati data dauki matakin kawo karshen rikicin makiyaya da manoman da ake ganin wasu daga cikin shugabanni na da hannu a ciki.
Kasar Chad na cikin kasahen yankin Sahel da ke fuskantar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da ke dada karuwa tare da sanadiyyar rasa rayukan mutane da yawa.
Cikin shirin za a ji yadda hukumomi a Najeriya ke kiran 'yan ƙasa su rungumi zaman lafiya da girmama juna. A Ghana kuwa kokawa ake yi game da yadda rigingimun Najeriya za su shafi tattalin arzikin ƙasar. A Nijar tarurruka aka yi don daidaita al'amaura gabanin zaɓuka.
Bayan labaran duniya, za a ji karin bayani kan taron sasanta manoma da makiyaya tsakanin Najeriya da Nijar a jihar Diffa na Nijar. Wani atisayen hadin gwiwa tsakanin rundunar soji da ta 'yan sanda a Ghana ya sake karbo ikon yankin Volta sa'o'i kalilan bayan masu rajin kafa kasar Togoland sun karbe ikon yankin.
A cikin shirin za a ji cewa Annobar COVID-19 na neman haifar da mummunan tsaiko a aikin fidda adadin danyan mai da Najeriya ke fitarwa waje. Najeriya da Kamaru na laluben hanyar maganata ta'addanci ta kan iyakokinsu. a Nijar biyo bayan annobar corona, makiyaya sun koka da matsalolin kiwo musamman a kan iyakokin kasashen da ke makwabtaka da Nijar.
A cikin shirin akwai rahoto a kan sasanci a tsakanin makiyaya da manoma a Adamawan Najeriya da rahoto a kan sufurin jirgin ruwa a Legas da kuma rahoto a kan bikin al'ada da ake kira 'Yenandi' a Gaya Jamhuriyar Nijar da rahoto a kan kasuwanci da wayar salula a Kamaru.
A cikin shirin za ku ji cewar yayin da dalibai ‘yan makarantar Boko mazauna birine ke kwasar garabasar ilimi ta kafar radiyo da gidan talabijin a cikin dokar kulle, kungiyar matan fulanin Najeriya ta bayyana cewa ‘ya’yan makiyaya mazauna karkara na fuskantar koma baya a bangaren ilmin su saboda rashin kafafen sadarwa da wutar lantarki.
A cikin shirin akwai rahoto a kan yadda Nijar ke ci gaba da garkame 'yan fafutuka da rahoto a kan yadda a Najeriya aka mayar da fulani makiyaya saniyar-ware wurin yaki da coronavirus. Mun kuma kawo rahoto a kan ranar iyali ta duniya. Akwai labaran duniya.
A Najeriya gwamnatin Filato ta kaddamar da shirin killace dabbobi domin kiwo a wuri guda, a wani mataki na magance tashe tashen hankula tsakanin makiyaya da manoma.
Bayan kun saurari Labarun Duniya, za kuji rahoton afkuwar rikici tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Guri da ke jihar Jigawa a Najeriya.
A cikin shirin za ku ji cewa rikicin manoma da makiyaya na kara kamari a yankin Gaya na jamhuriyar Nijar wannan kuwa duk da matakan fadakarwa da ake ta yi kai a kai a kasar.
A zamanin rayuwarsa, Muhammadu Ibrahim Danfulani Mai tambola ya bada gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin fulani makiyaya da manoma da sada zumunta a tsakanin 'yan kungiyoyin zabi sonka na Afrika.
A cikin shirin za a ji a cigaba da kokarin neman mafita kan rikicin makiyaya da manoma, gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun amince da kaddamar da shirin inganta harkokin kiwo da ke da zummar tsugunar da masu sana'ar kiwon a jihohin yankin. A jamhuriyar Nijar kuwa jami'iyyar CDS Rahama ta cimma yarjejeniyar dinke barakar da take fama da ita.
A cikin shirin za a ji cewa kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya ta hada kai da jami'an tsaro a wani yunkuri na magance matsalar garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
A cikin shirin za a ji cewa matakin gwamnatin Najeriya na dakatar da shirin RUGA na samar da wuraren kiwo ga makiyaya na ci gaba da haifar da muhwara a kasar.
A cikin shirin za a ji bayan share tsawon kwanaki ana kace-nace kan shirin nan na RUGA a Najeriya wanda ya tanadi tsugunar da Fulani makiyaya a waje guda, gwamnatin kasar ta sanar da dakatar da shirin.
Kasar Chadi za ta farfado da kotun sojoji ada zimmar kawo karshen rigingimun manoma da makiyaya
Bayan labaran duniya, cikin shirin akwai rahotannin da suka hada da ta samar da matsuganai ga mutanen da matakin rushe-rushen gidaje da hukumomin jihar Legas a Najeriya suka yi.
Kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar na bayyana damuwarsu a game da yadda attajirai masu kudi ke sayen filayen da suke komawa mallakarsu abin da ke zaman cikas ga makiyaya a game da sha'ann kiwo.