Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi labaran duniya wanda a ciki aka ji cewar Iran ta zargi Isra'ila da kisan wani fitaccen masanin nukiliya na kasarta. Akwai kuma shirin Afirka a Mako wanda ke bita kan muhimman batutuwan da suka faru a nahiyar Afirka a wannan makon mai karewa.
A karon farko bayan sabunta dangantaka a tsakanin juna, jirgin fasinjan Hadaddiyar Daular Larabawa na Flydubai ya soma jigilar fasinjoji daga Isra'ila zuwa birnin Dubai a wannan Alhamis.
A cikin shirin zaku ji cewar Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da rusau din da Isra'ila ta yi a yankin Falasdinawa. Akwai sauran labarai da rahotanni masu kayatarwa.
Kasashen duniya na jinjina wa Sudan saboda dawo da hulda da ta yi da Isra'ila
Shirin ya kunshi labaran duniya da waiwayen wasu manyan batutuwan da suka wakana a nahiyar Afirka a wannan makon mai karewa. Sudan ta amince da sake dawo da hulda da kasar Isra'ila. ICC ta ja kunne game da rikicin kasar Guinea Conakry.
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soki Sudan bisa amincewar da ta yi da Isra'ila a matsayin abokiyar hulda. A wannan Juma'ar ce kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dawo da dangantaka a karkashin jagorancin Amirka.
Isra'ila za ta fara dawo da huldar da ke tsakaninta da hadaddiyar daular Larabawa
Shuwagabanni da al'ummomin kasashen Larabawa, na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan kulla alakar diplomasiyya tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Isra'ila.
A cikin shirin za ku ji cewar wasu Yahudawa tare da Palsadinawa sun yi zanga-zangar adawa da shirin firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na hade wasu yankunan Falalsniwan yamma da kogin Jodan da Isra'ila.
A cikin shirin za a ji cewa yau ake sa ran Firaiministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya aiwatar da shirinsa na mamaye kaso 30 cikin 100 na yammacin kogin Jordan, matakin da ka iya ja wa Falasdinawa babbar asarar karfin iko da suke da shi a yankin. A Tarayyar Najeriya kuwa darurruwan matasa ne suka fara tururuwa don rejistar sunayensu a tsarin nan na bada tallafi da horon kan sano’i wato N Power.
A cikin shirin za a ci cewar an taras da gawar Jakadan Chaina a Isra'ila a gidansa kwanaki kadan bayan da sakataran harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya gargadi kasar da ta daina saka jari a Chaina.
Mata sun shiga cikin hada-hadar sufurin kananan jiragen ruwa a yankin Niger Delta na Najeriya.
Kasashen duniya na ci gaba da bayyana matsayinsu kan shirin Shugaba Donald Trump na Amirka na zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, a yayin da MDD ta jaddada matsayinta na sansanta Isra'ila da Palasdinawa.
A cikin shirin za a ji rahotanni da labaran duniya, ciki har da matakin kasar Saudiya na ci gaba da mutunta dokar haramtawa 'yan Isra'ila shiga kasar.
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, muna tafe da rahotanni ciki har da na bikin tunawa da kisan kare dangi da gwamnatin kama karya ta 'yan Nazi ta yi wa Yahudawa a Jamus.
Bayan kun saurari Labarun Duniya, muna dauke da rahoton yadda firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya samu nasara a zaben shugabancin jam'iyyar Likud da ya gudana a kasar.
A cikin shirin bayan Labaran Duniya muna tafe da rahotanni da suka hadar da na yadda garin Bethlehem ke da muhimmanci ga mabiya addinai sakamkon kasancewarsa mahaifar Annabi Isa Al-Masihu. Akwai sauran rahotanni da kuma shirye-shiryen da muka saba gabatar muku.
A cikin shirin za ku ji cewa a bisa shiga tsakanin kasar Masar Isra'ila ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan Palasdinawa, sai dai kuma ko a wannan Alhamis sojojin Isra'ilan sun halaka wasu Palasdinawan a yankin Gaza.
Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a yankin Zirin Gaza bayan tsagaita awuta na dan wani lokaci da suka yi, sakamakon bukatar hakan daga kasar Masar.