Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A Jamhuriyar Nijar huldar da tashar DW ta kulla tare da wasu gidajen radiyoyi masu zaman kan, na taka babbar rawa wajen bai wa al’ummar kasar damar samun labarai da shirye-shiryen na DW cikin sauki ba tare da sun sha wahalar neman tashar ba.
A cikin shirin za a ji cewar shugaban gwamnatin Jamus Angela Markel ta tattauna ta wayar tarho da zababben shugaban Amirka Joe Biden inda ta taya shi murna da kuma jaddada kudirin karfafa hulda tsakanin nahiyar Turai da Amirka.
Kasashen duniya na jinjina wa Sudan saboda dawo da hulda da ta yi da Isra'ila
Shirin ya kunshi labaran duniya da waiwayen wasu manyan batutuwan da suka wakana a nahiyar Afirka a wannan makon mai karewa. Sudan ta amince da sake dawo da hulda da kasar Isra'ila. ICC ta ja kunne game da rikicin kasar Guinea Conakry.
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soki Sudan bisa amincewar da ta yi da Isra'ila a matsayin abokiyar hulda. A wannan Juma'ar ce kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dawo da dangantaka a karkashin jagorancin Amirka.
Yakin Iran da Iraki, guda ne daga cikin yake-yake mafi muni a Gabas ta Tsakiya. Yakin na shekaru takwas da aka yi amfani da makamai masu guba, ya halaka dubban mutane ya kuma raba kawunan al'umma bisa tafarkin akida.
Ziyarar ita ce irinta ta farko cikin tsukin shekaru 35, da wani shugaban kasar Jamus ya kai a Sudan, wanda a ziyarar shugaba Frank-Walter Steinmeier ya sha alwashin tallafa wa kasar.
A cikin shirin za a i cewa Nijar da Rasha na shirin bude wani sabon bababin hulda a fannoni dabam-dabam da suka hada da na cinikayya, tsaro da kuma diplomasiyya.
An dai sani akwai fahimta tsakanin Yoweri Museveni na Yuganda da takwaransa Paul Kagame na Ruwanda, amma an rufe iyakar kasashen biyu, hanyar da miliyoyin 'yan kasuwa da al'umma ke bi don hulda tsakanin kasashen.
Kasashen Jamus da Najeriya sun jaddada kudirin karfafa hulda a tsakaninsu inda ma a yayin ziyarar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kasashen biyu suka ratta hannu kan wasu yarjeniyoyi biyu na kasuwanci da kuma batun 'yan gudun hijira.
Hulda tsakanin China da Ruwanda ta kama hanya bayan da Shugaban kasar China Xi Jiniping ya gana da Paul Kagame na Ruwanda a ziyara da ya kai a kasar.
Cikin shirin za a ji a karon farko tun bayan shekaru 20, kasashen Habasha da Iritiriya sun dawo da zirga-zirgar jirage tsakaninsu bayan sasantawar da aka samu cikin 'yan makonnin da suka gabata.
Shirin ya kunshi labaran duniya wanda a ciki aka ji cewa shugaban kasar Iritiriya Isaias Afwerki ya fara ziyarar aiki a kasar Habasha a matakin kyautata hulda da juna. Baya ga llabarai, akwai shirye-shirye da suka hada da Ciniki da Masana'antu da Ji Ka Karu da Amsoshin takardunku sai kuma filin Wasikun Masu Sauraro.
Tsawon shekaru Afirka na zaman babbar kawar Palasdinu. Amma yanzu kasashen Afirka da dama na inganta hulda da Isra'ila. Sai dai sabon hadin kan na da nakasu.
Jamus na bukatar fadada huldarta a kasashen Afirka, wannan ya sa aka zabi kasar Ghana a matsayin kasar da za a kulla hulda da ita. Saboda haka ne ma shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yada zango a kasar Ghana.
Shugaban sashen Afirka na DW, Claus Stäcker, ya bayyana a cikin sharhin da ya yi cewa ba a cika damawa da matasa a Afirka ba duk da kwazo da shi. Wannan ya zo a daidai lokacin da muka kaddamar da sabon shirin Matasa Kashi 77.
A cikin shirin za a ji kungiyoyin kwadago, da ma'aikatan kafofin watsa labarai a Najeriya sun yi barazanar cewa daga yanzu duk wani gwamnan jihar da ya dauki matakin rushe wata kafar watsa labarai, za su janye hulda dashi.
Jamus na son shigar da kyawawan manufofinta na tallafa wa tsarin bunkasa kasashen Afirka a gaban babban taron kungiyar G20, manufoyin da ake kallo a matsayin buri mai cike da tsammani.
A kokarin kara karfafa hulda tsakaninta da kasashen Afirka, Jamus ta kaddamar da sabon shiri mai taken "Marshall Plan" da nufin tallafawa kasashen nahiyar.