Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Babu shakka tarihin Jamhuriyar Benin ba zai cika ba, ba tare da ambaton cinikin bayi ba, lokacin da shugabanni suka sayar da fursunonin siyasa ga Turawa. Yanzu kasar na kokarin sanyaya wahalar da aka sha a baya.
Za a ji cewa gwamnatin jihar Edo ta sa dokar hana fita a Benin babban birnin jihar byan kona ofishin 'yan sanda
Fiye da karni biyar bayan sarautarsa, gadon da Oba Ewuare ya bari na nan daram-dakau a cikin garin Benin. Ana tunawa da karfin ikonsa da kuma habaka fasahar sarrafa tagulla da ake cin amfani har yanzu.
Hukumomi a Najeriya sun bukaci rushe daukacin rumbunan ajiye kaya da ke a kan iyakar Najeriya da kasashen Benin da na Niger kafin kaiwa ga bude iyakokin da ke tsakanin kasashen.
Cikin shirin za a ji martani da kuma zanga-zangar da Amirkawa ke yi dangane da matakin Shugaba Trump kan Iran. Tsananin sanyi na gana wa mazauna jihar Sokoto azaba. Makiyayan Nijar na kokawa da matakin hana shiga kasarta da makwabciya Benin ta yi.
A cikin shirin za a ji cewar a kasar Guinea Konakry al'ummar na ci gaba da nuna adawa da yunkurin tazarce na shugaba Alpha Conde. A Najeriya kuma ministocin harakokin wajen kasashen Najeriya da Nijar da kuma Benin sun gudanar da wani taro kan batun rufe iyakar Najeriya da makobtanta.
Rufe kan iyakokinta da awasu kasashe makwabta da suka hadar da Nijar da Benin da Kamaru da Najeriya ta yi, ya haifar da matsaloli da tarin kalubale.
A karon farko madinka daga kasashen Senegal Yuganda da Benin sun baje kolin tufafi da sauran kayan kwalliya na Afirka a birnin Berlin. Wannan rukunin madinkan na Afirka na zamani na da burin daukaka martabar tufafin Afirka da sauya tunanin da duniya take da shi na fifita tufafin Turai idan ana maganar ado da kwalisa.
A cikin Shirin bayan Labaran Duniya, za ku ji cewa al'umma na nuna damuwa da fargaba dangane da matzakin da sifeto jana na 'yan sandan Najeriya ya dauka, na bayar da umurnin kame jagororin kungiyar IMN ta 'yan uwa Musulmi mabiya Shi'a. Akwai sauran rahotanni
Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar ya nemi shugaban Kasar Benin da ya tiso keyar Hama Amadou zuwa gida, wannan tsokaci ya janyo muhawara a kasar.
A cikin shirin za ku ji cewa kasar Benin ta haramta shigo da gurbataccen man fetir a wani mataki na neman kara inganta muhalli da kyautata lafiyar jama'a a kasar.
'Yan sanda sun kashe masu zanga-zanga biyu a jamhuriyar Benin
Za a ji kura ta lafa jamhuriya Benin bayan barkewar rikicin bayan zabe da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu
A wannan Lahadin ne al'umar jamhuriyar Benin ke gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki inda 'yan takara duk suka kasance na bangaren gwamnatin mai ci ba tare da 'yan takara daga bangaren adawa ba.
Za a ji 'yan adawa a jamhuriyar Benin na kokawa kan hanasu shiga takara a zabukkan 'yan majalisun kasar dake tafe
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, daga cikin rahotannin da muka tanadar muku akwai rahoto kan rikicin kasar Yemen ke shafar fararen hula musamman kananan yara.
Gwamnatin kasar Benin ta dauki matakin maido da hurumin nada shugabannin jami'o'in gwamnati a karkashin ikonta. Gwamnatin ta ce ta dauki wannan mataki ne a wani yinkurin na inganta tsarin tafiyar da jami'o'in.
Hukumomin tsaro a Faransa na tsare da attajin dan kasuwa kana dan kwangila Vincent Bollore wanda ya shahara a kasashen Afirka.
Duk da matakin sufeta janar na 'yan sandan Najeriya na soke wuraren binciken ababen hawa a manyan hanyoyin kasar, 'yan sandan sun ci gaba da tsayar da motoci suna karbar na goro.
A cikin shirin za a ji cewa hukumomin kasar Senegal sun kori babban dan gwagwarmayan nan Kémi Séba, dan asalin kasar Benin da ke yaki da takardar kudin CFA a yammacin Afrika, inda suka ce bisa dalilai na neman tayar da zaune tsaye a kasar.