Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa Amirka ta tabbatar da yariman Saudiyya da kitsa kisan gillar da aka yi wa dan jaridar nan Jamal Khashoggi, akwai kuma shirin Afirka a Mako.
A cikin shirin za a ji shirye shirye irinsu Ku shiga Kulob da Amsoshin Takardunku da shirin wasikun masu sauraro da Ciniki da Masana'antu.
A cikin shirin za a ji Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa duban al'umma da ke gudun hijira a yankunan gabashin Afirka ne ke fuskantar barazanar tsunduma cikin matsananciyar yunwa a wannan shekarar.
Shirin darasin rayuwa ya yi nazari kan yadda annobar corona ta haifar da mummunan illa ga rayuwar ma'aikatan gidajen kallo da yawon bude ido a wasu kasashen nahiyar Afirka.
Ko kun san cewa cin gyada na iya yin magani tare da bayar da kariya daga kamu wa daga cututtuka kamar su cancer dana hawan jini ko ciwon suga a sakamakon yadda sinadaran da take dauke da su suke daidaita jini?
A kasar Ghana ana fama da matsalar bara tsakanin kananan yara.
A cikin shirin za a ji cewa shuwagabannin Kungiyar Tarayyar Turai na taron kolin dakile yaduwar cutar corona da ke addabar nahiyar, a yayin da Jamhuryair Nijar ma'aikatar cikin gidar kasar ta yi karin haske kan boren da ake fuskanta tun bayan kammala zaben shugaban kasa zagaye na biyu.
A cikin shirin za a ji labarai da rahotanni daga sassan duniya, ciki har da matakin da kungiya mai safarar kayayyakin gwari daga arewa zuwa kudancin Najeriya ta dauka na shiga yajin aiki.
Matsalar rashin aikin yi ta jefa matasa cikin mumunan hali a tarayyar Najeriya, inda wannan yanayi ya sa wasu matasa 24 kwashe fiye da watani bakwai a gidan yari bayan sun ba da cin hanci don daukar su aikin dan sanda.
Hadaddiyar kungiyar masu safarar abinci da dabbobi daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya ta dakatar da harkokinta bayan karewar wani wa'adi da ta bai wa hukumomin Kasar kan wasu kokensu da suke son a magance.
Mahukuntan Nijar sun kame Janar Moumouni Boureima a yayin da ake farautar madugun adawan kasar Malam Hama Amadou wanda ya yi batan dabo. Wannan ya biyo bayan tarzomar bayan zabe inda aka samu asarar rai da ta dukiya.
Bayan labaran duniya za a ji cewa a kalla mutum uku ne suka mutu a wani zaftarewar kasar da ya auku a Indonesiya.
A cikin shirin za a ji yadda zanga-zanga bayan zabe ke ci gaba da gudana a Jamhuriyar Nijar.
A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji dan takarar jam'iyyar RDR Chanji ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar Nijar. 'Yan siyasar Najeriya irinsu Buba Galadima da ke adawa sun goyi bayan 'yan adawar Nijar a yayin da shugaban Najeriya ya ce an yi zaben Nijar cikin gaskiya da bin dokokin zabe. Za kuma ku ji cewa an katse intanet a Nijar saboda zanga-zangar adawa da sakamakon zabe.
Kiddiga ta nunar da cewa kaso 77 na al'ummar Afirka matasa ne masu jini a jika. Da dama dai daga wadannan matsa, na yin yunkurin samun sana'o'in da za su rinka yi domin su dogara da kansu.
A kan samu masu tabin hankali musamman ma mata, wadanda ake wa fyade su haihu a kuma bar su da yara ba tare da kulawa ba. Hakan ce ta sanya gwamnatin jihar Katsina da ke Tarayyar Najeriya, kai wadannan masu tabin hankali asibitoci domin kula da lafiyarsu da kuma ba su kariya daga masu cin zarafin nasu.
Da yawan matasa a kasar Hausa kan dogara da aikin gwamnati musamman wadanda suka yi karatun boko, abin da Nura Kofar Kaura mai sana'ar jari bola ya bayyana da gurgun tunani.
A cikin shirin za ku ji an kai harin roka a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya wanda ya yi sanadin rayukan mutum a kalla 10.