Mece ce makomar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a yanzu? | Siyasa | DW | 19.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mece ce makomar jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a yanzu?

'Yan kwanaki bayan nada sabon firaminista a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kamoun ya gaza kafa gwamnatin hadin kan kasa, ga kuma ballewar da Seleka ke ikirarin ta yi.

Mahamat Kamoun

Sabon firaminista Mahamat Kamoun

A yunkurinsa na warware kiki-kakar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, shugaban kasar Kwango kuma mai shiga tsakani a rikicin Afirka ta Tsakiya, Denis Sassou N'guesso ya kira wani taro tun a jiya litinin a birnin Brazaville, wanda ya hada 'yan siyasa da bangororin da ke rike da makamai don samun mafita.

A hukumance Michel Djotodia ne shugaban kungiyar ta Seleka amma bisa ga dukkainn alamu ba shi da cikakken iko a kan dukkannin mabiyansa. Ga misali a jajibirin sa hannu kan yarjejeniyar birnin Brazzaville da aka yi a karshen watan Yulin da ya gabata, bangaren siyasa na Seleka ya bada sanarwar soke wakilcin Mahamat Moussa Daphane da cewa ba shi ne wakilinsu ba a wajen taron. Habylah Awal kakakin tsohon shugaban kasar, Michel Djotodia, ya tabbatar da cewa kungiyar Seleka ta kunshi bangarori biyu tun farko, wato da na siyasa da ma soja.

Tilas ne a cika sharuddan da aka gindaya

A karshen tattaunawar da ke gudana a birnin Brazaville ana sa ran samun amincewar bangarorin da ke gaba da juna, don kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa, sai dai a cewar Habylah Awal kakakin Michel Djotodiya kungiyar Seleka ba za ta shiga duk wata gwamnati ba sai an cika wasu sharudda da za ta gindaya. Wadanda suka hada da wadanda ke kunshe a cikin yarjejeniyar N'djamena

Yarjejeniyar birnin N'djamena dai da kakakin shugaban Selekar ke magana akai ta tanadi cewa, za a raba madafun iko ne da shugabannin kungiyar ta Seleka, abin da da wuya gwamnatin rikon kwaryar ta amince da shi. Shi ya sa ake ganin cewa zai yi wuya jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar ta fita daga rikicin siyasa ta yadda sabon firaminista Mahamat Kamoun zai sami damar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa nan ba da dadewa ba.

Mawallafi: Salissou Issa
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin