1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Me ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango

July 18, 2009

Taƙaitaccen bayanin dalilin da ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/IsH0
Shugaba Joseph Kabila, na jamhuriyar dimokuraɗiyyar KwangoHoto: AP

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Jamilu Abdussalam daga jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi, wane dalili ne ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango? Yanzu kenan akwai ƙasashe biyu masu suna Kwango! A gaskiya abin na da rikitarwa! Dafatan za ku yi min cikakken bayani.

Amsa: To dama dai tun asali ƙasar sunanta jamhuriyar Kwango, tun kafin zamanin mulkin mallaka, to amma bayan da Turawan mulkin mallaka suka mamaye ƙasar sai suka sa mata suna jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango a ranar 1, ga watan Agustan, 1964, kuma an yi haka ne da nufin banbance ta da maƙociyarta wadda ita ma sunanta jamhuriyar Kwango.

Mobutu
Mobutu Sese Seko, tsohon shugaban Kwango, a lokacin tana amsa sunan ZayarHoto: AP

Yadda aka yi ta samu tsohon sunanta na Zayar kuwa ya faru ne a ranar 27 ga watan Oktoban 1971, a zamanin mulkin tsohon shugaba Mabutu Sese Seko. Kuma sunan ya samo asali ne daga yadda al'ummar ƙasar Potigal suke kiran kogin kwango da suna nzere ko nzadi, wato ma'ana "Kogi mai haɗiye sauran koguna." To amma bayan da aka gudanar da yaƙin Kwango na farko, wanda yai sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Mobutu a shekarar 1997, an sake mayar wa da ƙasar sunanta na zamanin Turawan mulki, wato jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango.

Ita dai jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango, ƙasar Faransa ce tai mata mulkin mallaka, kuma ta kansance ne a yankin tsakiyar Afirka. Ita ce ƙasa ta uku a girman taswira a nahiyar Afirka. Sannan kuma kamar yadda ƙiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya ya nunar, ƙasar na da yawan al'umma kimanin miliyan 66,020,000 wanda hakan ya ba ta iko zama ƙasa ta 19 a jerin ƙasashe mafiya yawan al'umma a duniya, kuma ta huɗu a yawan al'umma a Afirka, amma kuma a rukunin ƙasashen da suke magana da harshen faransanci a duniya ita ce ƙasa ta farko a yawan al'umma.

Denis Sassou Nguesso
Shugaba Denis Sassou Nguesso, na jamahuriyar KwangoHoto: AP

Babbar hanyar da ake iya rarrabe ƙasashen kwangon guda biyu ita ce, ita wannan kwangon da muke batu akai a kodayaushe ana ambatonta ne da jamhuriyar ɗimokuraɗiyyar Kwango, ko a ce DR Kwango, ko DRC, ko RDC, ko kuma a kira ta da Kwango-Kinshasa, wato a jingina mata sunan babban birninta na Kinshasa. Saɓanin ɗaya Kwango ɗin da ake mata laƙabi da Kwango-Brazzaville.

Shi dai wannan suna "Kwango" Suna ne na "Kogin Kwango", har ila yau kuma akan kira shi da Kogin Zayar (Kuma sunan ya samo asali ne daga sunan wata ƙabila da ake kira Bakongo). jamhuriyar dimokuraɗiyyar Kwango dai, ƙasa ce da ta sha amsa sunaye da dama a tarihi, inda akan ce mata 'yantacciyar ƙasar Kwango, ko Kwangon Beljiyom, ko Kwango-Kinshasa, ko kuma Zayar.

Duk da cewa ƙasar ta jamhuriyar dimokuraɗiyyar ta kasance ne a yankin tsakiyar Afirka, to amma fa ta fuskar harkokin tattalin arziki da kuma ɓangaranci, ta alaƙanta kanta ne da ƙasashen kudancin Afirka kasancewar ita mamba ce a ƙungiyar bunƙasa ƙasashen kudancin Afirka wato (SADC).

Ƙasar ta yi iyaka da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Sudan daga arewa, sannan kuma ta yi iyaka da Uganda, da Rwanda, da Burundi ta fuskar gabas, har ila yau ta yi iyaka da Zambiya da Angola ta ɓangaren kudu, ta ɓangaren arewa kuwa ta yi iyaka ne da takwarar tata jamhuriyar Kwango.

Mawallafi: Abba Bashir

Edita: Muhammad Nasir Awal