MDD za ta rage yawan dakarunta a Kwango
March 31, 2017Talla
Wakilan kwamitin sulhu sun kada kuri'ar rage yawan dakarun rundunar da kishi bakwai cikin dari wanda daga addadin sojojin da jami'an tsaro dubu 19 da 'yan ka da ake da su a Kwangon ,ya koma dubu 16.Gesine Ames wata 'yar kasar Jamus kwararrariya a game da yankin tsakiya na Afirka ta ce akwai bukatar tura dakarun na MONUSCO zuwa Kwangon domin tabbatar da tsaro a yankunan da ake yin tashin hankali.