'Yanci da walwalar jama'a na gamuwa da cikas a duniya
February 25, 2019Talla
A lokacin da yake jawabi a wajen taron sakataran MDD António Guterre ya yi kiran da a kawo karshen wariyar jinsi da rashin juriya kuma ya ce da sannu a hankali 'yancin dan Adam na samun koma baya a kasashen duniya da dama. Kana ya yi Allah wadai da karuwar 'yan mulkin populiste abin da ya ce hadari ne da kuma ci gaba da yada jawaban kiyaya a kafofin sada zumunta.