MDD ta yi Allah wadai da harin Kunduz | Labarai | DW | 04.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta yi Allah wadai da harin Kunduz

Farmakin da Amirka ta kai wa wani asibitin kungiyar Doctors Without Borders a Afganistan inda ta hallaka mutane 19 wasu 37 suka jikkata lamari ne na aikata alaifin yaki

A cewar daraktan gudanar da ayyukan asibitin Bart Janssens, abun kaito shi ne sojojin Amirka da na Afganistan duk an fada musu ana kai wa asibitin hari, amma sama da mintuna 30 Amirkawan suka ci gaba da luguden wuta kan. Daraktan asibitin mai bada agajin gaggauwa kyauta, yace wannan asibitin ya yi shekaru hudu yana aiki a Kunduz, kuma ba karamin asibiti bane, domin girmansa yafi filin kwallon kafa fadin, kuma sau da dama suka yi magana da masu gaba da juna kan asibiti. Don haka ya ce kungiyar ta Doctors Without Borders, ba za ta taba lamunta ace wai kuskure ne Amirka ta yi ba.