1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu tallafin $2.4 bn don magance yunwa a Afirka

May 25, 2023

Damina guda biyar da aka yi a jere ba tare da kasashen sun sami ruwan saman da za su shayar da amfanin gona ba ne suka kara jefa mutanen yankin kahon Afirka cikin yunwa tare da hallaka miliyoyin dabbobi.

https://p.dw.com/p/4RnDM
Hoto: AMANUEL SILESHI/AFP

Majalisar Dinkin Duniya, MDD,  ta sanar da samun tallafin kusan Dala miliyan 2,500 domin magance matsalar yunwa a kasashen da ke yankin kahon Afirka da ke fama da matsanancin fari a yayin da suke shaida karuwar zafin rana a kusan kowacce shekara.

Sanarwar ta MDD ta ce za a yi amfani da wadannan kudade domin ceto rayukan mutane kusan miliyan 32 da ke kasashen Habasha da Kenya da Somaliya, tana mai gargadin cewa har yanzu kudin da aka tara ba su kai Dala miliyan 7,000 da take nema domin magance matsalar karancin abinci a tsakanin mutanen wannan yanki ba.

Tun daga shekara ta 2020, kasashen yankin kahon Afirka irinsu Djibouti da Habasha da Eritrea da Kenya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Sudan suka fara dandana 'kamfar ruwan saman' da ba su shaida irinsa ba a cikin shekaru 40.