1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta nuna damuwa kan rincabewar rikici a Kwango

February 14, 2024

Kwamittin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa kan yadda rikici ke kara kamari a gabashin Jamhuriyar dimokradiyar Kwango.

https://p.dw.com/p/4cOUN
DR Kongo | M23 Rebellen
Hoto: Arlette Bashizi/REUTERS

A baya-bayan nan fada dai ya kara kazanta a tsakanin 'yan tawayen M23 da kuma dakarun kasar. A cikin sanarwar da kwamittin ya fitar, ya yi Allah wadai da hare-haren da 'yan tawayen ke kara zafafa kai wa a farkon wannan watan a kusa da birnin Goma.

Kasar Kwangon da gwamnatocin kasashen yammacin Turai gami da kwararru a MDD na zargin 'yan tawayen da samun goyon bayan kasar Ruwanda, zargin da gwamnatin Kigali ta musanta.

Ko a karshen makon da ya gabata ne dai 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da rashin tsaro a kasar. Masu boren sun yi ta kona tutocin kasashen Amirka da Beljiyam a gaban ofisoshin jakadancin kasashen yammacin Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya da ke fadar gwamnatin kasar, Kinsasha. Ana dai zargin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da suka shafe shekaru 25 a kasar da gaza kawo karshen ayyukan ta'addanci.