MDD ta kaddamar da gagarumin neman taimakon kan agajin jinkai | Labarai | DW | 08.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta kaddamar da gagarumin neman taimakon kan agajin jinkai

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan tabarbarewar harkokin jinkai a kasashen duniya da ake samun tashe-tashen hankula da sauran bala'o'i.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci samun kudaden da suka kai dala milyan dubu-20, kwatankwacin Euro milyan dubu-18, daga gwamnatoci domin mayar da martani kan rikice-rikice da ake samu gami da bala'oi.

Hukumomin majalisar masu kula da jinkai sun samu kimanin rabin abin da suke bukata a wannan shekara, kuma rashin samun abin da ake nema ya hsafi harkokin abinci, samar da matsugunai, da kuma kula da kiwon lafiya na miliyoyin wadanda suke bukata.

Stephen O'Brien jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi bayani kan cewa mutane milyan 125 za su bukaci taimakon jinkai a shekara mai zuwa ta 2016. A ciki ana bukatar kai wa ga fiye da milyan 87 da rabi.