1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren MDD ya kadu da matsalar Venezuela

Abdoulaye Mamane Amadou
February 24, 2019

Babban Sakataren na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna damuwarsa da jin irin halin da kasar Venezuela ta ke a ciki tare da nuna tsananin bukatar warware rikicin cikin runwan sanyi.

https://p.dw.com/p/3E0hU
Äthiopien Gipfeltreffen der Afrikanischen Union in Addis Abeba Antonio Guterres
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Babban sakatare na MDD  Antonio Guterres ya yi kira ga bangarorin da ke rikici a kasar Venezuela da su sanya wa zukatansu ruwan sanyi.

Ko a ranar Juma'ar da tagabata Antonie Guterres ya yi wata ganawa da jami'an huldar diflomasiyyar kasashen Amirka da Venezuela kan lalabo hanyar samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji, inda ya matsa kainmi kan ci gaban da ake da tayar da tarzoma yana mai fatan samun masalaha a cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba.

Sannu a hankali dai rikicin kasar Venezuela na kara tsananta, tsakanin magoya bayan madugun 'yan adawa Juan Guaido da jami'an sojan da ke yiwa ga Nicolas Maduro. Ko a ranar asabar da tagabata wasu mutane sun hallaka da dama kuma suka ji rauni, biyo bayan taho mu gaman da magoya bayan madugun 'yan adawar suka yi da sojojin da ke biyayya ga Nicolas Maduro.