1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta yi kira a tsagaita wuta a Libya

Abdullahi Tanko Bala
July 5, 2019

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci tsagaita wuta a Libya tare da yin Allah wadai da harin jiragen sama a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da Tripoli wanda ya hallaka mutane da dama.

https://p.dw.com/p/3Lfj8
UN-Weltsicherheitsrat tagt zum Libyen-Konflikt
Hoto: picture-alliance/Xinhua News Agency/Li Muzi

Harin da aka kai a ranar Talata kan sansanin 'yan gudun hijira dake Tajoura a gabashin Tripoli ya hallaka mutane 53 da jikkata wasu 130. Birtaniya wadda ta tsara jadawalin da ya yi Allah wadai ta bukaci komawa teburin tattaunawa tare da martaba haramcin makamai a Libya.

Majalisar Dinkin Duniya  ta yi kira a gudanar da bincike mai zaman kansa domin tantance wanda ke da alhakin kai hari kan sansanin da ke dauke da yan gudun hijira 600 yawancinsu daga kasashen Afirka. Gwamnatin Libya ta zargi bangaren Khalifa Haftar mai hamaiya da kai harin, zargin kuma da Haftar din ya musanta.

Kungiyar lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutane kimanin dubu daya aka kashe tun bayan da Haftar ya kaddamar da farmaki a watan Afrilu don karbe iko da birnin Tripoli daga hannun gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke marawa baya. Fadan dai ya sa mutane fiye da dubu dari daya kauracewa gidajensu wanda kuma ya kara jefa Libya cikin tashin hankali.