MDD ta bukaci bincike na kasa da kasa a Siri Lanka | Labarai | DW | 16.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD ta bukaci bincike na kasa da kasa a Siri Lanka

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi kafa kwamitin bincike na kasa da kasa domin tantance cin zarafin da aka samu lokacin yakin basasan kasar Siri Lanka.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi karin haske kan cin zarafin da aka samu lokacin yakin basasan kasar Siri Lanka, da dubban mutane suka bace, sannan ta nemi kasar ta gudanar da bincike da kuma sasanta al'uma. Babban jami'in majalisar mai kula da kare hakkin dan Adam Zeid Ra'ad Al Hussein ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland cewa ana bukatar bincike na kasa da kasa, saboda kotunan kasar ba za su iya tantance lamarin baki daya ba.

Kasar ta Siri Lanka ta shafe shekaru 26 na yakin basasan kafin murkushe 'yan tawayen Tamil Tigers a shekara ta 2009, kuma kimanin mutane 100,000 suka hallaka. Tuni Shugaba Maithripala Sirisena ya yi alkawarin hukuntan wadanda suka take hakkin dan Adam lokacin yakin basasan.