MDD ta amince da rundunar G5 Sahel | Duka rahotanni | DW | 22.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

MDD ta amince da rundunar G5 Sahel

Kwamitin sulhun ne ya yi na'am da matakin kafa rundunar kawancan kasashen Afirka biyar na yankin Sahel  ko G5 Sahel wacce za ta yaki kungiyoyin 'yan ta’adda na masu kaifin kishin Islama a yankin mai iyaka da hamada.

Illahirin mambobi 15 na kwamitin sulhun MDD ne dai suka amince da kudirin neman  kafa wannan rundunar kawance ta G5 Sahel, wacce kasashen Mali Moritaniya Nijar, Chadi da Burkina Faso, ke son kafawa a bisa bukatar kungiyar Tarayyar Afirka, domin fuskantar da kansu kalubalen tsaron da yankin na Sahel yake fama da su. Musamman a sakamakon ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi dama sauran kungiyoyin masu fataucin makamai da kwaya da dai sauran masu aikata muggan laifuka, wadan da suka mamaye yankin na Sahel. Da yake jawabi a zauran MDD jim kadan bayan kada kuri’ar amincewa da matakin kafa rundunar ta G5 Sahel, jakadan kasar Faransa a MDD Francois Delattre ya bayyana gamsuwarsa da matakin yana mai cewa:

"Wannan kudiri da muka dauka zai taimaka sosai ga wannan tsari da nahiyar Afirka ta fiddo da kanta, na yakar ayyukan ta'addanci. Kuma matakin zai taimaka sosai wajen karfafa wa kasashen nahiyar Afirka a burinsu na iya  daukar matakan tsaron nahiyarsu da kansu"

Da farko dai kasar Faransa dama kasashen na G5, sun so a ce rundunar ta kasance a karkashin ikon MDD, to amma wasu kasashe kamar su Birtaniya da Amirka suka nuna adawarsu da hakan, domin suna ganin zai bukaci tallafin kudade daga MDD a daidai lokacin da majalisar ke iya fuskantar matsalar kudi, musamman bayan matakin tsuke bakin aljihu da kasar Amirka ta dauka tun daga lokacin hawan gwamnatin shugaba Trump. To sai dai jakadan kasar ta Faransa a MDD Francois Delattre, ya bayyana fa'idar taimaka wa Afirka a cikin wannan kokowa ta yaki da ta'addanci ga sauran kasashen duniyar.

"Ba za mu bari ba yankin Sahel ya zamo mafakar kungiyoyin 'yan ta'addan duniya. Tabbatar da tsaron lafiyar yankin Sahel tamkar tsaron lafiyar kasashenmu ne mu kanmu, ba wai na G5 kawai ba. Dan haka ya zamo dole mu kama mu yi wannan aiki a tare"

Kudurin Kwamitin sulhu ya bukaci babban magatakardar MDD Antonio Guterres, cewa nan da watannin biyu masu zuwa da ya gabatar da rahoto na kan matsalolin da rundunar ta soma fuskanta, dama gabatar da shawarwari na inganta ta dama yiwuwar samar mata gudunmawar kudi daga MDD. Ko da shike tun a farkon wannan wata na Yuni, Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da taimakawa rundunar da kudi miliyan 50 na Euro. Kuma kungiyar ta bukaci sauran kasashen duniya su yi koyi da ita. Kudurin Kwamitin sulhu na MDD, ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba za a shirya wani taro na neman taimakon kudi daga kasashen duniya domin tallafa wa rundunar ta G5 Sahel. To amma da yake jawabi jim kadan bayan da kwamitin sulhun MDD ya amince da kudurin kafa rundunar ta G5 , jakadan Kasar Mali a MDD Issa Kanfourou, ya ce a shirye kasashen nasu suke su dauki nauyin rundunar ta G5 Sahel, kafin samun duk wani dauki daga waje.

"Mu muna son gaggautawa, domin sun 'yan ta'adda fa ba sa jira. Kuma a yanzu haka ina mai tabbatar muku da aniyar kasashenmu na bai wa maradansu kunya, domin shugabannin kasashenmu sun dage a kan ganin sun dauki nauyin wannan runduna da kansu kafin zuwan tallafin kasashen duniya"

A watan Maris din da ya gabata ne dai, shugabannin hafsoshin sojan kasashen na Sahel, suka tsaida cewa rundunar kawancan ta G5 Sahel, za ta kunshi mutun dubu biyar zuwa dubu 10 da suka hada da sojoji da 'yan sanda da kuma fararan hula. Kuma za a girke ta a birnin Bamako na kasar Mali, kana za ta kasance a karkashin jagorancin Janar Didier Dacko, tsohon babban hafsan hafsoshin sojan kasar ta Mali.

Sauti da bidiyo akan labarin