MDD: Kashedi kan karuwar yunwa a kasashen Afirka
July 30, 2025
Rahoton da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya guda biyar suka fitar, ya nunar da cewa sama da mutum guda cikin biyar a nahiyar Afirka da ke da yawan al'umma kimanin miliyan 307 na fama da karancin abincin mai gina jiki a shekra ta 2024 da ta gabata. Hakan na nufin yiwuwar matsalar yunwa, ta ta'azzara fiye da shekaru 20 din da suka gabata.
Wani rahoto na Yanayin Matsalar Abinci mai Gina Jiki a Duniya ya nunar da cewa, adadin al'ummar duniya da ke fuskantar matsalar yunwa ya ragu. Rahoton ya ce kimanin mutane miliyan 673 ko kuma kaso takwas da digo biyu cikin 100 na yawan al'ummar duniya ne suka fuskanci matsalar yunwa a duniya a shekarar da ta gabata ta 2024, idan aka kwatanta da kaso takwas da digo biyar cikin 100 da suka fuskanci matsalar ta yunwa a shekara ta 2023.
A hirarsa da tashar DW kan wannan batu, shugaban Asusun Bunkasa Ayyukan Noma na Kasa da Kasa IFAD, Alvaro Lario ya nunar da cewa:
"Gagarumar matsalar karancin abinci na afkuwa ne sakamakon rikici, mun fuskanci matsalar rikice-rikice mafi girma a shekaru 10 da suka gabata."
Gibin da ke tsakanin farashin kayan abinci a duniya da hauhawar farashi da aka samu a duniya a watan Janairun 2023 ya sanya farashin abinci da ke da sinadaran gina jiki tashin gauron zabi, abin da ya fi shafar kasashe matalauta. Abincin da ake samarwa ya yi wa adadin al'ummar da ake da su a wadannan kasashe karanci, sakamakon karuwar al'ummar da ake samu. Rikicin da kasashen Sudan da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke ciki, ya kara sanya al'umominsu cikin halin tasku.
Cikin wani jawabinsa na faifen bidiyo da aka sanya a yayin taro kan tsarin abinci a kasar Habasha, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa: "Yunwa na barazana ga samun daidaito a nan gaba, tana kuma barazana ga zaman lafiya." Wani abun damuwar ma wasu kasashen Afirka bashi ya yi musu katutu, abin da kwararru suka bayyana da wanda ke dakile samar da abinci ga al'umma. Kamar yadda shugaban Asusun Bunkasa Ayyukan Noma na Kasa da Kasa IFAD, Alvaro Lario ya nunar.
"Guda cikin manyan kalubalen da kasashen Afirka da dama ke fuskanta shi ne, biyan basussuka. Suna biyan kudin ruwa mai yawa a kan bashin da ake binsu, wanda yawansa ya kai tsakanin kaso 10 zuwa kaso 25 cikin 100. A bayyane yake karara, yana dakile yiwuwar zuba jari. Wannan wani abu ne da muke son yin nazarinsa a mataki na kasa da kasa, yadda za mu taimaki kasashe da dama a kan dimbin bashin da ake binsu ko kuma biyan kudin ruwa na basussukan da ake binsu."
Kungiyoyin da ke yaki da matsalar yunwa, sun yi kira da a samar da shugabanci na gari da kuma samar da isassun kudin da tsarin ci-gaba, domin dogaro da kai a fannin samar da abinci. Kan wannan batu, shugaban IFAD Lario ya ce:
"Yana da matukar amfani kasashe su mayar da hankali wajen zama masu dogaro da kansu, domin kananan manoma da dama ba wai kawai su samar da abinci ba har ma su samu damar sayar da shi a kasuwanni. Zuba jari zai zamo matakin farko, idan muna son magance talauci da yunwa a yankunan karkara."
Rahoton na SOFI ya nunar da cewa adadin mutanen da ba sa iya samun lafiyayyen abinci ya ragu a yankunan Asiya da Latin Amurka da Caribbean da Amurka ta Arewa da kuma Turai, sai dai ya karu a kasashen Afirka daga kaso 64 da digo daya cikin 100 a 2019 zuwa kaso 66 da digo shida cikin 100 a 2024. Hakan na nufin daga mutane miliyan 864 zuwa biliyan daya. A wasu kasashen kamar Najeriya, farashin abinci ya karu musamman mai sinadaran gina jiki. A gidajen marasa hali yana wahalar samuwa, abin da ke kara yawan barazanar yunwa da karancin abinci mai gina jiki.