Mayakan Tigray sun yi watsi da rahotannin tada hankali
November 7, 2021Talla
Mayakan kabilar Tigrai (TPLF) da kawayensu sun shafe shekara guda suna gwabza yaki da gwamnatin Ethiopia, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da jefa wasu da dama cikin mawuyacin hali.
Firaiminista Abiy Ahmed, wanda ya lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya ta 2019, ya tura sojoji cikin yankin Tigray a watan Nuwambar 2020 don kawar da kungiyar ta TPLF kan zarginsu da kai hari kan sansanonin soji.
Sai dai kungiyar ta TPLF da kawayenta, ta sha ikirarin samun nasarori da dama a cikin 'yan makonnin da suka gabata, inda suka yi ikirarin kwace garuruwa masu tazarar kilomita 400 daga babban birnin kasar.