1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan jihadi sun kamo hanyar zaman lafiya

Ramatu Garba Baba
February 7, 2019

Gwamnatin kasar Mali ta ce ta cimma nasara da kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai, inda mayakan jihadi akalla 5,000 suka amince da sanya hannu kan shaidar yarjejeniyar ajiye makamai.

https://p.dw.com/p/3CtRA
Al-Kaida im Islamischen Maghreb
Hoto: AFP/Getty Images

Fiye da 600 ne suka ajiye makamansu nan take. Mayakan dai sun hada da masu fafutukar jihadi da manyan mambobi na kungiyoyi na masu gwagwarmaya da makamai da ayyukansu ya janyo asarar rayuka da dukiya.

Firai ministan Malin, Soumeylou Boubeye Maiga da ya sanar da kaddamar da shirin a watan Disambar bara,  ya yaba da matakin ganin yadda suka aka samu hadin kai a tsakanin bangarorin biyu kafin ma cikar wa'adin da gwamnati ta gindaya, ya ce ci gaba ne da zai taimaka ainun a kokarin da ake na samar da tsaro a ciki dama kewayen kasar ta Mali.