May ta tsallake kuri′ar yankan kauna | Labarai | DW | 13.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

May ta tsallake kuri'ar yankan kauna

Firaministar Birtaniya Theresa May ta kai labari bayan da 'yan majalisar dokoki na bangaren jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya suka kada mata kuri'ar yankan kauna.

Daga cikin 'yan majalisa 317, guda 200 sun amince ta ci gaba da jagoranci a matsayin firaminista, yayin 117 suka nemi ta sauka daga mukamin nata. Wannan dai ya nunar da cewa jam'iyyar ba za ta sake fuskantar barazana ba ta fuskar shugabanci nan da shekara guda.

Sai dai Firaminista May ta fada wa 'yan majalisar cewa, za ta ajiye mukamin nata kafin babban zabe da za a yi a 2022. Amma kafin nan za ta mayar da hankali kan wadannan batutuwa: "Aiwatar da shirin fitar Birtaniya daga EU kamar yadda al'umma suka zaba da hada kan 'yan kasa da aiki da zai amfani kowane dan Birtaniya."

Babban kalubale da ke gaban May dai na zama na yadda shugabanni daga kungiyar Tarayyar Turai ciki kuwa har da Angela Merkel ta Jamus, suka nunar da cewa babu sauran wata kwaskwarima ga yarjejeniyar da suka kulla da Birtaniya a shirinta na fita daga EU da za su amince da ita.