Mauritius: Shekaru 50 da samun ′yanci | Siyasa | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mauritius: Shekaru 50 da samun 'yanci

Badakalar cin hanci na neman yin awon gaba da kujerar Shugaba Ameenah Gurib-Fakim ta Tsibirin Mauritius, a dai-dai lokacin da tsibirin ke bikin cika shekaru 50 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya.

Shugabar Tsibirin Mauritius Ameenah Gurib-Fakim

Shugabar Tsibirin Mauritius Ameenah Gurib-Fakim

Bayan shekaru 150 na mulkin mallaka na Turawan Birtaniya ne kasar Mauritius ta samun 'yancin kanta a ranar 12 ga watan Maris na 1968, kana a ranar 12 ga watan Maris na 1992 wannan tsibiri ya zama Jamhuriya. Al'ummar wannan kasa ba su fi miliyan daya da dubu 200 ba amma kuma sun shafe kwanaki suna bukukuwa don nuna irin ci-gaban da suka samu a cikin shekaru 50 a fannin tattalin arziki da kuma siyasa. Hasali ma dai sabanin tsibirin Madagaska da ke makotaka da ita inda ake samun juyin mulki na soja, Mauritius ta yi fice a fuskar samun daidaito tsaknin jam'iyyun siyasa domin tafiyar da mulki a cewar Alex Vines shugaban sashen Afirka a Chatham House.

Wuraraen shakatawa da bunkasar tattalin arziki

Kasa mai tarin wuraren shakatawa da kuma kabilu da addinai daban-daban

Kasa mai tarin wuraren shakatawa da kuma kabilu da addinai daban-daban

Baya ga wuraren shakatawa da bakin teku da ta mallaka, Tsibirin Mauritius ya kunshi kabilu daban daban da 'yan asalin Indiya suka kasance kashi 70 cikin 100 na al'umma yayin da sauran masu tsatso da bakaken fata na afirka su kasance kashi 30 cikin 100. Sabanin sauran kasashen afirka, addinin Hindu ne ke da rijaye fiye da Kiristanci da kuma Islama. A wasu lokuta ana samun rashin fahimta tsakanin addinai daban-daban wanda ke zama baban kalubale ga kasar. Sai dai a fannin tattalin arziki, tsibirn Mauritius ya tsere wa sa'o'insa na kasashen Afirka saboda kudin da kowanne dan kasar ke samu ya ninka na sauran 'yan nahiyar so hudu zuwa biyar. A yanzu haka ana sanyan tsibirn na Mauritius a sahun kasashe da ke da matsakaicin karfi. Baya ga noman rake da kuma yawon bude ido, tsibirn na Mauritius ya yi fice a harkar hada-hadar kudi na bankuna kana guda daga cikin wuraren da ake boye kudi saboda gudun biyan haraji. Tsibirin dai na shan yabo daga gidauniyar Mo Ibrahin a fannonin gudanar da mulki da bunkasar tattalin arziki.

 

Sauti da bidiyo akan labarin