Mauritaniya na shirin zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 21.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mauritaniya na shirin zaben shugaban kasa

An fitar da Jaddawalin zaben shugaban kasa a Mauritaniya, inda masu tsayawa takara zasu ajiye takardun su kafin 7 ga watan Mayu mai zuwa.

Hukumomi a Mauritaniya sun fitar da jaddawalin zaben shugaban kasa a wannan Litinin din (21.04.2014), inda zagayen farko na zaben zai gudana ne a ranar 21 ga watan Yuni mai zuwa, sannan zagaye na biyu, zai gudana a ran 5 ga watan Yuli. Labarin ya fito ne daga kanfanin dillancin labaran kasar na AMI.

Kudirin dai ya bada izini ga dukkan yan kasar ta Mauritaniya masu bukatar tsayawa takara a wannan zabe, da suyi kokarin ajiye takardun takarar su kafin ran 7 ga watan Mayu mai zuwa, kuma za'a buda yakin neman zabe a ranar 6 ga watan Yuni, har ya zuwa ran 19 ga watan na Yuni tsawon kwanaki 13 kenan.

An dai fitar da jaddawalin zaben shugaban kasar yan kwanaki kalilan kafin wani zaman tataunawa da za'ayi tsakanin yan adawar kasar da gwamnati.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu